Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane dan wasa ne zai maye gurbin Ansu Fati kafin ya warke?
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
Dan wasan Barcelona Ansu Fati zai yi jinyar wata hudu, bayan raunin da ya yi a karawa da Real Betis a Gasar La Liga a karshen mako.
Tun ranar Litinin likitoci suka yi masa aiki, sannan suka tabbatar cewar zai yi jinyar wata hudu kafin ya dawo taka leda.
A cikin watan Nuwamban ba zai buga wa Barcelona wasa da kungiyar za ta ziyarci Atletico Madrid a gasar La Liga da wanda za ta je ta fafata da Dynamo Kiev a Champions League.
Da kuma wanda Barcelona za ta karbi baƙuncin Osasuna a gasar La Liga ranar Lahadi 29 ga watan Nuwamba.
Cikin watan Disamba kuwa matashin dan wasan ba zai buga wa kungiyar ta Camp Nou fafatawa bakwai ba.
Su ne wanda Barcelona za ta yi da Ferencvaros a Champions League da Cadiz a La Liga da Juventus a Champions League da wanda za ta je Levante a La Liga.
Sauran sun hada da karawa da Valencia da Valladolid da kuma Eibar a La Liga.
Ana sa ran ɗan kwallon zai koma taka leda ko dai a karshen watan Fabrairu ko kuma cikin watan Maris.
Fati ya buga wa Barcelona wasa 10 ya kuma ci kwallo biyar, haka kuma ya yi wa Spain karawa hudu ya ci kwallo ɗaya a kakar bana.
Tsawon lokacin da dan wasan zai yi jinya ya zama wajibi koci Ronald Koeman ya samu dan kwallon da zai maye gurbinsa.
Dan wasan na buga gurbin gaba daga gefe ne a salon wasannin da yake yi a shekarar nan.
To ko wane dan kwallon ne zai maye gurbinsa a Barcelona.
Antoine Griezmann
Dan wasan tawagar Faransa ba zai so sake buga gurbin gaba daga gefe ba, domin wurin da ya buga ne a bara amma ya kasa taka rawar gani da wasu ke ganin Barcelona ta yi barnar kudinta.
To sai dai bai da zabi idan koci ya zabi ya sake buga wurin, domin hakan zai bashi damar buga wasanni da yawa kenan da watakila ya koma kan ganiyarsa.
Kawo yanzu ya buga wa kungiyar wasa 10 ya ci kwallo biyu, ya kuma yi wa Fransa karawa uku ya zura kwallo uku a raga a bana.
Pedri
Pedri shi ma yana taka rawar gani a kakar bana kamar yadda Fati ya nuna kansa a gasar La Liga da Champions League da kuma Barcelona.
Mai shekara 17 ya buga wa kungiyar wasa 10 ya kuma ci kwallo biyu, wanda ya koma Camp Nou da taka leda daga Las Palmas.
Ousmane Dembele
Bayan da Dembele ya sha jinya a kakar bara, ya dawo da karfinsa a bana, wanda kawo yanzu ya buga wa Barcelona wasa takwas ya ci kwallo uku.
Dan kwallon na buga bangaren hadu, saboda haka zai iya buga gurbin gaban daga bangaren hagun ba tare da matsala ba.
Trincao
Dan kwallon tawagar Portugal mai cin kwallo ya koma Barcelona a bana daga Braga, kuma wannan ne lokacin da ya kamata ya nuna kansa.
Kawo yanzu ya buga wa Barcelona wasa 10 har da Champions League biyu, sai dai har yanzu bai ci kwallo ba.
Rashin Ansu Fati zai iya samun damar nuna kansa kan bajintar da zai yi a kungiyar a shekarar nan.
Philippe Coutinho
Dan kwallon Brazil ya shiga cikin 'yan wasan da Koeman ke amfani da su yana kuma nuna kwarewarsa a bana.
Coutinho ya buga wa Barcelona wasa shida a kakar shekarar nan ya kuma ci kwallo biyu.
Sai dai da zarar an maida shi buga gefe, Barcelona za ta kasa cin moriyar kwallon da ya kware buga wa daga tsakiya.
Martin Braithwaite
Dan kwallon tawagar Denmark ya yi wa Barcelona wasa biyar kawo yanzu har da Champions League karo daya, kuma yana bukatar samun yin karawa da yawa domin ya nuna abinda zai iya yi.
Dan wasan na buga gurbin mai cin kwallo, zai kuma amince ya shiga karawa daga baya ya buga gurbin gaba daga gefe karkashin Koeman.
Konrad de la Fuente
Fuente dan kasar Amurka, mai buga kwallo ne daga hagun fili, wanda ake gani zai dace a gwada shi a gurbin da Fati ya bari domin yin jinya.
Sai dai kuma bai da kwarewa kuma bai buga wasa ko daya ba, aikin zai yi masa wahala matuka.
Wasa biyar da ke gaban Barcelona:
Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga
- Atl Madrid da Barcelona
Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League
- Dynamo Kiev da Barcelona
Lahadi 29 ga watan Nuwamba La Liga
- Barcelona da Osasuna
Laraba 2 ga watan Disamba Champions League
- Ferencvaros da Barcelona
Lahadi 6 ga watan Disamba La Liga
- Cadiz da Barcelona