Philippe Coutinho: Mai taka leda a Barcelona zai yi jinya

An wallafa

Dan kwallon Barcelona, Philippe Coutinho ba zai buga wa kungiyar Gasar Champions League da za ta kara da Juventus ranar Laraba ba, sakamakon raunin da ya yi.

Tsawon jinyar da dan wasan mai shekara 28 zai yi, ya dogara da girman raunin da ya ji kamar yadda Barcelona ta sanar.

Dan kwallon tawagar Brazil ya buga minti 90 a Gasar La Liga karawar hamayya ta El Clasico da Real Madrid ta yi nasara da ci 3-1 a kan Barca ranar Asabar a Camp Nou.

Tsohon dan wasan Liverpool ya buga wasannin aro a kakar 2019/20 a Bayern Munich.

Sai dai dan wasan ya buga wa Barcelona karawa biyar da aka fara tamaula da shi karkashin kocii Ronald Koeman.

Wasa biyar nan gaba da Barcelona za ta fafata:

Laraba 28 ga Oktoba Champions League

  • Juventus da Barcelona

Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga

  • Alaves da Barcelona

Laraba 4 ga watan Oktoba Champions League

  • Barcelona da Dynamo Kiev

Asabar 7 ga watan Nuwamba La Liga

  • Barcelona da Real Betis

Lahadi 22 ga watan Nuwamba La Liga

  • Atl Madrid da Barcelona