Real 3-2 Inter: Karon farko da Real ta yi nasara a Champions League a bana

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Kwallon da Rodrygo ya ci ya bai wa Real Madrid damar doke Inter Milan - karon farko da kungiyar ta ci wasa a Gasar Champions League ta bana.

Real ta yi nasara ne da ci 3-2 ta kuma fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema, sannan kyaftin Sergio Ramos ya ci ta biyu, kuma na 100 da ya zura a raga a Real Madrid.

Sai dai kuma ba a jima ba Inter ta zare kwallo ta hannun Lautaro Martinez, sannan Ivan Perisic ya ci na biyu, inda karawar ta rukuni na biyu ta koma 2-2.

Rodrygo ne ya ceci Real Madrid, bayan da ya ci na uku, bayan da ya Vinicius Jr ya ba shi kwallon..

Da wannan sakamakon Real tana da maki hudu iri daya da na Shakhtar Donetsk ta biyu a teburi da tazarar maki daya da Borussia Monchengladbach mai jan ragama.

Inter Milan ce ta karshe da maki biyu a mataki na hudu.

A ranar ta Talata Gladbach ta doke Shakhtar 6-0, kuma Alassane Plea ne ya ci uku rigis a wasan, kuma kwallayen da ya fara ci kenan a Champions League.

Real da Inter sun kara sau tara a Gasar Zakarun Turai kafin wasan da suka kara a Spaniya ranar Talata, inda Madrid ta ci wasa uku, ita kuwa Inter ta yi nasara a biyar, suka yi canjaras daya tal.

'Yan wasan da kocin Real, Madrid, Zinedine Zidane ya fuskanci Inter Milan a Alfredo Di Stefano.

'Yan wasan Real Madrid da za su fafata da Inter:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron bayas: Sergio Ramos da R. Varane da Marcelo da F. Mendy da kuma Santos.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Asensio da Lucas da Jovic da kuma Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.

Karon farko da Zidane da Conte suka fuskanci juna a matakin masu horar da tamaula

Zinedine Zidane ya taka rawar gani a lokacin da ya buga kwallon kafa kuma daya ne daga koci-koci da suka lashe kofina a wannan karnin.

Dan kasar Faransan da Bob Paisley da kuma Carlo Ancelotti, su ne ke da tarihin lashe Champions League sau uku a tarihi.

Tsakanin 1996 da 2001, Zidane ya taka leda kaka biyar a Juventus tare da Antonio Conte kocin Inter na yanzu da za su fuskanci juna a matakin masu horar da kwallon kafa.

Jerin wasa da aka kara tsakanin Real Madrid da Inter Milan a Gasar Zakarun Turai

Talata 3 ga watan Nuwambar 2020 Champions League

  • Real Madrid 3-2 Inter

Laraba 25 ga watan Nuwambar 1998 Champions League

  • Inter 3 - 1 Real Madrid

Laraba 16 ga watan Satumbar 1998 Champions League

  • Real Madrid 2 - 0 Inter

Laraba 22 ga watan Afirilun 1981 European Cup

  • Inter 1 - 0 Real Madrid

Laraba 8 ga watan Afirilun 1981 European Cup

  • Real Madrid 2 - 0 Inter

Laraba 1 ga watan Maris 1967 European Cup

  • Real Madrid 0 - 2 Inter

Laraba 15 ga watan Fabrairun 1967 European Cup

  • Inter 1 - 0 Real Madrid

Laraba 20 ga watan Afirilun 1966 European Cup

  • Inter 1 - 1 Real Madrid

Laraba 13 ga watan Afirilun 1966 European Cup

  • Real Madrid 1 - 0 Inter

Laraba 27 ga watan Mayun 1964 European Cup

  • Inter 3 - 1 Real Madrid

Ranar Talata Inter ta tashi 2-2 a gida da Parma a wasan mako na shida a Gasar Serie A ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba, kuma Inter tana ta shida a kan teburi da maki 11.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 16, bayan da ta doke Huesca 4-1 a fafatawar mako na takwas a dai ranar ta Asabar.

Real ce kan gaba a lashe kofin Zakarun Turai na Champions League da 13 a tarihi, kuma hudu daga ciki ta lashe ne a kaka bakwai da suka wuce.

Kuma tun lokacin da aka sauya fasalin gasar, Real ce tilo da ta lashe kofin karo uku a jere, ta kuma buga wasan karshe a Champions League sau 16.

Bajintar da Inter ta yi a Spaniya

Inter ta taka rawar gani a filin wasa na Santiago Bernabeu, inda ta lashe kofi biyu a Spaniya - Intercontinental Cup a 1964 da kuma Champions League a 2010.

Wasa na karshe da kungiyar ta Italiya ta kara da Real shi ne a 1998 da suka fafata a birnin Sevilla.

Sai dai wasan da za su buga ranar Talata za a yi shi ne a Alfredo Di Stefano wato filin Real take gudanar da atisaye saboda gyare-gyare da ake yi a Bernabeu, filin da Inter ta yi wasa na karshe da Real a UEFA Cup a shekarar 1986.

Wasannin Real Madrid biyar nan gaba da za ta fafata:

Lahadi 8 ga watan Nuwamba La Liga

  • Valencia da Real Madrid

Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga

  • Villarreal da Real Madrid

Laraba 25 ga watan Nuwamba Champions League

  • Inter da Real Madrid

Lahadi 29 ga watan Nuwamba La Liga

  • Real Madrid da Alaves

Talata 1 ga watan Disamba Champions League

  • Shakhtar da Real Madrid

Karawa biyar da Inter Milan za ta fuskanta nan gaba:

Lahadi 8 ga watan Nuwamba Serie A

  • Atalanta da Inter

Lahadi 22 ga watan Nuwamba Serie A

  • Inter da Torino

Laraba 25 ga watan Nuwamba Champions League

  • Inter da Real Madrid

Asabar 28 ga watan Nuwamba Serie A

  • Sassuolo da Inter

Talata 1 ga watan Disamba Champions League

  • Borussia M'gladbach da Inter