Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Corono virus: Rodrigo ya killace kansa, bayan hulda da mai annobar
Dan kwallon Leeds United wanda ta saya mafi tsada a bana a tarihin kungiyar, Rodrigo Moreno ya ce ya kamu da cutar korona.
Dan kwallon tawagar Spaniya, mai shekara 29, bai buga Gasar Premier League ba ranar Litinin da Leicester City ta doke Leeds, bayan da ya killace kansa.
Dan wasan ya fada a kafar sada zumunta a Instagram cewa ya yi hulda ta kud-da-kud da wani daga cikin iyalai da ya kamu da annobar.
Haka kuma Rodrigo ba zai buga Gasar Premier League ba ranar Asabar da Leeds United za ta ziyarci Crystal Palace.
Ranar Litinin Premier League ta ce ta samu mutun hudu da cutar korona, bayan gwajin 'yan wasa da koci-koci da jami'an kungiyoyi 1,446 da ta yi.
Ta gudanar da gwajin ne tsakanin Litinin 26 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba.