Lionel Messi: Kyaftin din Argentina zai buga karawa da Dynamo Kyiv

Asalin hoton, Getty Images
Ronald Koeman ya yi watsi da batun cewar Lionel Messi yana da wahala juyawa a fannin kwallon kafa.
Barcelona za ta karbi bakuncin Dynamo Kyiv a wasa na uku-uku a rukuni na bakwai a Gasar Champions League ranar Laraba.
Tsohon kocin Barcelona, Quique Setien ne ya ce kyaftin din Argentina ya ba shi wahala a lokacin da ya gudanar da aiki a Camp Nou.
"Ban amince da kalaman Setien ba, amma yana da damar fadar ra'ayinsa kan yadda ya gudanar da aiki, ina kuma girmama hakan'' in ji Koeman.
A cikin watan Agusta Messi ya bukaci barin Barcelona a bana, daga baya batun ya bi ruwa, kuma yanzu ya ci gaba da murza leda a Spaniya.
"Messi dan kwallon ne mai kyau kuma fitatce a duniya,'' kamar yadda Koeman ya ce. "Na hangin burinsa, sai dai dan wasa ne mai saukin kai.
Ranar 17 ga watan Agusta aka kori Setien, kwana uku bayan Bayern Munich ta casa Barcelona 8-2 a Champions League, inda Koeman ya karbi jan ragamar kungiyar.
Barcelona ta fara kakar bana da kafar dama a Champions League bayan da ta je ta doke Juventus da kuma Ferencvaros. Yanzu haka ita ce ta daya a kan teburin rukuni na bakwai.
Sai dai kungiyar da Koeman ke jan ragama tana ta 12 a teburin La Liga na shekarar nan, ba ta ci wasa hudu ba a gasar a jere, har da wanda Real Madrid ta yi nasara a kanta da ci 3-1 ranar 24 ga watan Oktoba.
Dynamo Kiev na da maki daya a wasa biyu na Champions League, sai dai ita ke jan ragamar teburin Premier a Ukraine da tazarar maki hudu tsakaninta da Shakhtar Donetsk.









