Barcelona: Wasa biyar za ta fafata a cikin watan Nuwamba

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Kungiyar Barcelona za ta kara a wasa biyar a cikin watan Nuwamba har da guda biyu a Gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Kawo yanzu Barcelona ta ci wasa hudu daga takwas da ta fafata a kakar bana, inda ta yi nasara biyu a La Liga da kuma biyu a Champions League.

Sai dai kawo yanzu Barca ta yi wasa hudu a jere a Gasar La Liga ba tare da yin nasara ba, inda ta yi canjaras biyu da rashin nasara biyu.

Barcelona ta fara doke Villareal da ci 4-0 a wasan bude La Ligar bana ranar 27 ga watan Satumba, sannan ta je ta ci Celta Vigo 3-0.

Daga nan ne Barcelona ta yi 1-1 da Sevilla a Camp Nou a Gasar La Liga, sannan ranar 17 ga watan Oktoba Getafe ta yi nasara a kanta da ci 1-0.

Haka kuma Barcelona ta yi rashin nasara a gida da ci 3-1 a hannun Real Madrid a karawar El Clasico, sannan ta je Alaves da kyar da gumin goshi ta tashi 1-1.

Barcelona wacce ta buga wasa shida tana ta 12 a teburin La Liga da maki shida, bayan buga karawar mako na takwas a gasar ta Spaniya.

To sai dai kuma kungiyar ta Spaniya ta lashe wasa biyu a jere na cikin rukuni a Gasar Champions League da ta kara.

Barca ta fara da yin nasara a kan Ferencvaros da ci 5-1 ranar 20 ga watan Oktoba a Camp Nou, sannan ta doke Juventus 2-0 a Italiya ranar 28 ga watan na Oktoba.

Da wannan sakamakon kungiyar ta Spaniya ta hada maki shida a wasa biyu tana ta daya a kan teburin rukuni na bakwai.

Sai Juventus ta biyu da maki uku, sannan Dinamo Kiev ta uku da maki daya iri daya da wanda Ferencvarosi keda shi.

Ranar Laraba Barcelona za ta karbi bakuncin Dinamo Kiev a wasa na uku-uku a cikin rukuni a gasar Champions League ta bana.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar Zakarun Turai sau takwas, inda Barcelona ta yi nasara biyar ita kuwa Dinamo Kiev ta ci wasa uku.

Wasannin da ke gaban Barcelona a cikin watan Nuwamba.

Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League

  • Barcelona da Dynamo Kiev

Asabar 7 ga watan Nuwamba La Liga

  • Barcelona da Real Betis

21 ga watan Nuwamba La Liga

  • Atl Madrid da Barcelona

24 ga watan Nuwamba Champions League

  • Dynamo Kiev da Barcelona

29 ga watan Nuwamba La Liga

  • Barcelona da Osasuna