Liverpool da Arsenal: Abubuwan da za su faru karawar kungiyoyin a Anfield

An wallafa

Ranar Litinin Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na uku a gasar Premier League ta bana ta 2020-21.

Fafatawa tsakanin kungiyoyin biyu a ko da yaushe ta hamayya ce da zarar sun hadu ba sai a gasar Premier League ba.

Liverpool mai rike da kofi ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta ci Leeds United ta kuma je Stamford Bridge ta doke Chelsea ta hada maki shida kenan.

Ita ma Arsenal kawo yanzu tana da maki shida a wasa biyu, bayan da ta yi nasara a kan Fulham da kuma West Ham.

Arsenal ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta lashe Community Shield, kuma a kan Liverpool ta yi nasara, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1.

Wasannin da kungiyoyin suka kara kafin fara gasar Premier League ta bana:

2020/2021

Community Shield Asabar 29 ga Agustan 2020

Arsenal1 - 1Liverpool

2019/2020

Premier League Laraba 15 ga Yuni 2020

Arsenal2 - 1Liverpool

EFL CUPLaraba 30 ga Oktoban 2019

Liverpool5 - 5Arsenal

Premier League Asabar 24 ga Agusta 2019

Liverpool3 - 1Arsenal

Duk yadda za a yi sai an samu maki a wasan

Ko dai Liverpool ta yi nasara a kan Arsenal ta hada maki uku a wasa uku jumulla tara kenan ta ci gaba da haska fitilar kokarin da za ta yi a kakar bana, ko kuma Gunners ta hada maki uku ta fayyace cewar a bana da ita za a yi rububin lashe kofin Premier League na bana, ba wai neman gurbin Europa kamar yadda da kyar ta samu matakin bayan yin nasara a kan Chelsea a FA Cup.

Ko kuma kungiyoyin su tashi canjaras ko kuma kunnen doki ko fiye da hakan da zai sa a raba musu maki daidai a tsakaninsu.

To sai dai rabon da Gunners ta doke Liverpool a Anfield tun bayan 2-0 da ta yi nasara a gasar Premier League ranar 2 ga watan Satumbar 2012, kuma Lukas Podolski da Santi Cazorla ne suka ci mata kwallayen.

Ko Aubameyeng zai ci Liverpool?

Bai dade ba kyaftin din Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da zama a Emirates, kuma hakan ya faranta ran duk wani magoyin bayan Arsenal ganin kwarewa da bajinta da dan kwallon ke nunawa tun zuwansa Ingila da taka leda daga Bundesliga.

Sai dai kuma wasa hudu ya fuskanci Liverpool a gasar Premier, amma bai zura kwallo a raga ba, kuma ya samu damarmaki biyar da ya kasa amfana a karawar baya da ya buga.

Watakila a karawar ranar Litinin kyaftin din tawagar Gabon ya bai wa mara da kunya.

Ko Fermino zai zura kwallo a ragar Arsenal?

Liverpool kan fuskanci kungiya da fitattun 'yan wasanta da suka kware wajen cin kwallo, kuma babu wanda zai so likkafarsa ta yi sama kamar Roberto Firmino.

Dan wasan ya ci Arsenal kwallo takwas, kuma ita ce ya fi yawan zura wa kwallaye a sauran kungiyoyin Premier League a sana'arsa ta kwallon kafa.

A wasa hudu da ya buga a Premier a Anfeld, Firmino ya fara zura kwallo a ragar Gunners.

A kakar bara ce kadai da dan kwallon Brazil bai ci Arsenal a Anfield ba, sai da ya buga kwallo ma ya bugi turke saboda rashin rabo.

Saboda haka Firmino zai nuna kokarin da zai yi a bana tun daga fafatawa da Arsenal har da kwallayen da zai iya ci a kakar 2020-21.

A wasan farko da Liverpool ta yi da Leeds Mohamed Salah ya ci kwallo uku rigis, shi kuwa Sadio Mane biyu ya zura a ragar Chelsea a Stamford Bridge.

Abin tambaya kwallo nawa Firmino zai ci Arsenal a Anfield a wasan Arsenal, ko kuma Gunners din ba za ta bari ya motsa ba a wasan?

Wasanni shida da Liverpool za ta buga nan gaba:

EFL CupAlhamis 1 ga Oktoba 2020

  • Liverpool da Arsenal

Premier League Lahadi 4 ga Oktoba 2020

  • Aston Villa da Liverpool

Premier League Lahadi 17 ga Oktoba 2020

  • Everton da Liverpool

Premier League Asabar 24 ga Oktoba 2020

  • Liverpool da Sheff Utd

Premier League Asabar 31 ga Oktoba 2020

  • Liverpool da West Ham

Premier League Asabar 7 ga watan Nuwamba 2020

  • Manchester City da Liverpool

Karawa shida da Arsenal da ta fafata nan gaba

EFL CupAlhamis 1 ga Oktoban 2020

  • Liverpool da Arsenal

Premier League Lahadi 4 ga Oktoba 2020

  • Arsenal da Sheff Utd

Premier League Asabar 17 ga Oktoba 2020

  • Man City da Arsenal

Premier League Asabar 24 ga Oktoba 2020

  • Arsenal da Leicester

Premier League Asabar 31 ga Oktoba 2020

  • Man Utd da Arsenal

Premier League Asabar 7 ga Nuwamba 2020

  • Arsenal da Aston Villa

Karawar da aka yi tsakanin Liverpool da Arsenal

Liverpool ta yi nasarar cin Arsenal wasa hudu a Premier League a gida, karawar da ta taka rawar gani a Anfield, tun bayan bakwai da ta doke Gunners har zuwa 1998.

Arsenal ta yi nasara a kan Liverpool cikin watan Yuni a karawa 10 a Premier League da canjaras hudu da rashin nasara biyar.

Arsenal za ta iya yin nasara a kan Liverpool a jere a Premier karon farko tun bayan Satumbar 2012.

Sai dai kuma lokacin da Gunners ta yi nasara a kan Liverpool tuni kungiyar ta lashe kofin Premier League na 2018-19.

Kwazon Liverpool

Liverpool ta yi nasara a wasa na farko a gasar Premier bara, kuma na uku da ta ci shi ne na Arsenal 3-1 a gida.

Babu kungiyar da ke rike da kofin Premier League ta ci wasa uku a jere a kakar gaba, tun bayan Manchester United a kakar 2011-12.

Wasa 60 da Liverpool ta yi a gida ba tare da an doke ta ban shi ne na uku a bajinta a gasar Ingila, bayan Chelsea mai 86 a kakar 2004-08 da ita kanta Liverpool mai 63 tsakanin 1978-80.

Kungiyar ta Anfield ta ci karawa 35 a jere a Premier League a gida tun daga 0-0 da ta yi da Manchester City cikin oktoban 2018.

Mo Salah ya ci kwallo 26 a Anfield daga 33 da ya zura a raga a gasar Premier League goals.

Kokarin da Arsenal ta yi

Arsenal za ta iya cin wasanni uku na farkon Premier League a karon farko tun bayan nasara biyar a kakar 2004-05.

Gunners ta yi nasara a wasan biyun farko a bara daga baya ta ci fafatawa biyu daga 13 da canjaras bakwai da rashin nasara hudu.

Arsenal za ta iya nasara a wasa hudu a jere a Premier a karon farko a bana, tun bakwai da ta ci daga Agusta zuwa Oktoban 2018.

Arsenal ba ta yi nasara a karawa 27 a Premier League da ta yi a waje ba, tsakanin manya kungiyoyi shida na sama tun doke Manchester City 2-0 a Janairun 2015.

An kuma zura mata kwallo 61 a wasa 27 din da canjaras 10 da rashin nasara 17.

Alexandre Lacazette ya ci kwallo hudu a wasa shida baya a Premier League, sai dai rabon da ya zura kwallo a raga a Premier tun ukun da ya ci a jere a Fabrairun 2019.

Mikel Arteta zai iya zama koci na farko a Arsenal da zai ci wasa a waje idan sun je Liverpool tun bayan kwazon Tom Whittaker a Disambar 1947.

Koci tara ne suka kasa yin abin azo a gani a irin wannan lokacin, inda takwas suka sha kashi.

Liverpool ce ke rike da kofin Premier na bara

Liverpool ce ta lashe kofin Premier League na bara kuma na farko tun bayan shekara 30. Jurgen Klopp ya taka rawar gani matuka, to ko bana kungiyar ta Anfield za ta iya kare kambinta?

A bara Liverpool ta kafa tarihi da dama a fannin kwallon kafar Ingila, watakila ta dora a bana ko kuma ta ji ana yi a makwabta.