Diogo Jota: Liverpool ta amince ta sayi ɗan wasan Wolves a kan £45m

Diogo Jota

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jota ya zura kwallo 44 a wasanni 131 da ya murza wa Wolves
    • Marubuci, Daga Mandeep Sanghera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa

Liverpool ta amince ta sayi ɗan wasan gaban Wolves Diogo Jota a kan yarjejeniyar da za ta kai £45m idan aka hada da 'yan tsarabe-tsarabe.

Kungiyar ta dauki matakin sayen dan wasan Portugal mai shekara 23 bayan Liverpool ta sayi dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara daga Bayern Munich.

A wata yarjejeniayr ta daban, Wolves na shirin sayo dan wasan Netherlands mai shekara 18 Ki-Jana Hoever daga Liverpool.

Ana sa ran Wolves za ta biya £9m kan Hoever, kodayake akwai yiwuwar kara masa £4.5m na alawus-alwus da kuma kashi 15 na kudin darajar dan kwallo.

Jota ya je Wolves a kakar 2017-18 a matsayin aro, amma daga baya ta saye shi a kan £12.8m a shekarar 2018.

Ya murza mata leda sau 131, inda ya zura kwallo 44, ciki har da kwallo uku-uku a wasa daya na gasar Europa Linda suka doke Besiktas da Espanyol.

Jota zai zama dan wasa na uku da Liverpool ta saya a bazarar bayan Alcantara kan £20m da kuma dan wasan Girka Kostas Tsimikas a kan £11.7m.