Precious Orji: 'Yar Najeriya da ta yi fice a duniya wurin ɗaga kayan nauyi

Precious Orji with her 2019 Paralympic gold medal

Asalin hoton, Para Powelifting

    • Marubuci, Daga Debola Adebanjo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Sport, Nigeria
  • An wallafa

Wannan shi ne burin Josephine Precious Orji, wadda ta kasance gwarzuwar Najeriya wurin ɗaga nauyi a gasar Olympics ta nakasassu wato Paralympics da kuma kafa tarihi a duniya.

Rayuwar Orji ta sauya sannu a hankali a karo na biyu a 2001, lokacin da ta ziyarci wurin motsa jiki a yankin da ta fito na Owerri a jihar Imo, domin soma gwada daga nauyi a karon farko na rayuwarta.

Sa'o'i biyu da soma hakan sai ta bai wa kanta mamaki: "Sai na ji ina son kai wa ƙololuwa a gasar."

Wannan ya kasance ƙwarin gwiwa ga matar mai shekara 41, wadda ta rasa ƙafafuwanta sakamakon kamuwa da cutar polio tun tana yarinya.

Jajircewa, baiwa ta musamman da kwazon da ta rika nunawa da kuma taimakon da ta samu daga gwamnatin jiha da ta tarayya sun taimaika mata wajen cimma burinta a gasar Paralympics ta 2016 a birnin Rio na Brazil.

Tun daga wannan lokaci ta haife jaririnta na biyu da kuma fuskantar koma-baya da dama amma wannan bai sa ta karaya ba wajen jajircewa da cimma burinta a wasan da take da sha'awa a kai tun 2001.

''Na daga nauyi 70kg a rana ta farko, na ji hakan da sauki kuma ban ji komai ba," ta shaida wa BBC Sport Africa.

"Kocin ya ce bai taɓa ganin wanda ya ɗaga 50kg ba a karon farko."

Wasan ɗaga nauyi na nakasassu na ganin yadda masu gasar ke daga nauyi cikin salon mamaki.

"Koci Lucky Ibe ya shaida mani zan zama gwarzuwa, kuma zan hau jirgi na zagaye duniya domin halartar manyan gasa," in ji Orji.

"Na kasa barci ina dauke da wadanan nauyi a cikin mafarkina a wannan daren, don haka na koma gida na ajiye aikina na rugumi atasaye."

Ƴar shekara 22 a wannan lokaci, Orji na tattare da jajircewar yin nasara da cimma burinta wanda ya kai ga ta ajiye aiki washe garin ranar domin rugumar sabon babi na rayuwar da ta zaba.

Tana aiki ne a matsayin ƙwararriyar kwamfuta a wani wuri mai hada-hada da ake harkar intanet, aikin da take da ƙwarewa a kai, tana jin dadi da kasancewa fitacciya a tsakanin abokan aikinta.

Wannan shi ne mafarin burinta da zai ba ta damar cimma abin da ta sanya gaba, tana da ƙwarin-gwiwa sosai na ganin ta kai matakin da take mafarki duk da cewa ta gamu da ƙalubale da ba a rasawa.

Abubuwan da ta cimma a yanzu shi ne lashe zinare a gasar nakasassu ta Paralympics a 2016 a Rio a bangaren ɗaga nauyi, wanda shi ne burinta tun da jimawa.

"Na ji kamar na tashi tsaye na tattaka a wannan ranar, na tashi daga keken guragu na taka sayyada ta," a cewarta.

"Mutane daga wasu kasashe na murna, an riƙe ni, ana ta neman daukar hoto da ni, ana tambayar na bayar da rigata, sannan na saka musu hannu ko buga tambari ko hatimi a fuskokinsu da sauran abubuwa.

"Na tuna irin fitattun mawakan nan - na ji kamar na zama irinsu, ban iya barci ba a wannan daren."

Rukunin da Orji ta haska a Rio shi ne kusan na karshe a Rio kuma zinaren da ta lashe ya kasance na takwas ga tawagar Najeriya kuma na shida da aka taɓa lashewa a ɗaga nauyi a Paralympics cikin shekara hudu.

Atisaye da sadaukarwa

Precious Orji in action

Asalin hoton, Hiroki Nishioka/World Para Powerlifting

Zinaren da Orji ta samu bai zo mata da sauki kamar shekara 15 da suka gabata ba lokacin da ta soma ɗaga nauyi, sai dai ta ce jajircewa da yawaita aitsaye ba kakkautawa da hukumar daga karfe ta yi masu ce sirrin.

"Mun shafe wata shida a sansani, ana horar da mu kamar sojoji, jikina ya yi ƙarfi kamar dutse," a cewarta.

"Ana kulawa da mu da biyan mu alawus a tsawon kwanakin, yanayin wurin babu laifi."

Yayin da wasu tawagogin Najeriya da masu wasan motsa jiki suka shirya zanga-zanga da shirya yajin aiki saboda a biya su kudaden alawus kan nasararsu ta duniya Orji na cikin wadanda suka yi nasarar.

Bayan wasannin, gwamnan jihar Imo - inda aka haife ta - na wannan lokacin Rochas Okorocha ba wai kawai ya yaba wa nasarorinsu ba, ya kuma alkawarta ba su tukwicin kudi.

"Ba bakon abu ba ne taimaka wa mutane masu nakasa da bukata ta musamman, 'ƴan wasan motsa jikin Imo sun lashe kambu kuma yi musu kyauta ba wani abu ne," kalaman Okorocha kenan, wanda yanzu sanata ne, a tattaunawarsa da BBC Sport Africa.

Goyon bayan ya wuce bayar da tukwici ga wadanda suka yi nasara a jihar domin an kai matsayin da gwamnatin na ƙarfafawa masu nakasa gwiwa domin cimma burikansu.

Gwagwarmayar da ta kai ga nasara

Precious Orji

Asalin hoton, Hiroki Nishioka/World Para Powerlifting

Tun wannan nasarar abubuwa sun sauya yadda suke tafiya ga Orji.

Ba ta samu damar lashe gasar duniya karo na biyu a Mexico a 2017 ba, saboda lokacin ta haifi 'ƴarta ta biyu.

Da kuma zabin mutum guda a kowanne rukuni a matsayin wanda zai wakilci kasa a gasar, hakan na nufin gurbi ya kasance abin da ake nema ruwa a jallo saboda rashin daidaito.

"Na rasa karfina, ban ji dadin hutun jego ba, saboda ya kasance dole na koma wata uku da haihuwa, ina zub da jini wani lokaci idan ana atisaye.

"Na shiga cikin yanayi na babu sauki, har yanzu ina fama da kaina, wani lokaci ina rashin lafiya wanda a baya ba na yi."

Ta shawo kan wadannan kalubale da sake gina kanta da wakiltar Najeriya a 2019 a gasar Paralympics da aka yi a Kazakhstan da kuma samun gurbi a gasar da za a gudanar a Tokyo.

Sai dai abubuwa ba su kasance yadda aka tsara ba bayan tasgaro da aka samu daga manajan tawagar, yanayin da ya jefa ta cikin yanayi na fadi tashin samun kambu.

Bisa kuskure ya shaida wa jami'ai cewa za ta soma ne da ajin 125kg, ma'ana za ta kasance a rukuni na B, an rage mata matsayi.

Taƙaita mata adadin da za a ba ta damar ɗagawa na nufin ba za ta iya shiga gasar da sa'aninta ba.

"Suna nan ana nunawa a jikin allo a matsayin mai rike da kambun duniya, amma kuma an jefa ni a rukunin B, na ji takacin abin, ba na son shiga gasar," a cewarta.

"Amma ya zame mani dole na kare matsayina duk da cewa an yi mun zarra, abin kun ya ne.

"A karon farko a tarihi na dawo babu abin da na samu, ya kasance abin kunya a gare ni.

'Amma ina yin wannan ne saboda sunana da kuma yarana su san cewa ga rawar da mahaifiyarsu ta taka.''

Precious Orji on stage at the 2019 World Para Powerlifting Championships in Kazakhstan

Asalin hoton, HIROKI_NISHIOKA

Bayanan hoto, Precious Orji ba ta lashe komai ba a gasar daga nauyi da aka gudanar a shekarar 2019 ta World Para Powerlifting Championships in Kazakhstan

Nauyi mafi girma da Orji ta taba ɗagawa na 143kg ya kasance kasa da kilo 17 kan wanda ta kafa tarihi a kai kuma rukuni na hudu ya fi dacewa da haka, gasa ta farko da ake dawowa gida babu kambu.

Ta daga nauyi iri guda da wanda Randa Mahmoud da ta lashe tagulla a Masar, wadda aka bai wa gurbi da ke kasa saboda rashin nauyin jikinta.

Nauyin da take ɗagawa ya ba ta gurbi a gasar Paralympics ta Tokyo da aka dage zuwa 2021 saboda annobar Covid-19, kodayake ba ta da tabbacin ajin da za ta wakilta a cikin tawagar har yanzu.