Nawal El Moutawakel: 'Yar tseren Morocco da ta kawo sauyi a kasashen Larabawa

Nawal El Moutawakel wins the 400m hurdles in the 1984 Olympics

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, El Moutawakel ta tsallake layi da tazara mai nisa har ta yi zaton almara ce
    • Marubuci, Daga Victoire Eyoum
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Sport
  • An wallafa

Idan ke mace ce 'yar Moroko sannan kin cika shekara 36 da haihuwa a halin yanzu, to an sanya maki suna Nawal.

Saboda nasarar Nawal El Moutawakel ta ranar 8 ga watan Augustan 1984 yayin gasar Olympics ta birnin Los Angeles da ke da matukar muhimmanci ga Sarkin Moroko Hassan na II, wanda har ta kai ya bayar da umarnin sauya wa duk yarinyar da aka haifa a wannan rana suna. Wannan shi ne labarinta.

Dukkan nasarar ta musamman ce. Amma wasu, na cika fiye da wasu, watakila saboda su sakamako ne na jumillar nasarorin ga mutum.

Wannan shi ne lamarin da ke tattare da nasarar Nawal El Moutawakel a shekarar 1984 yayin gasar Olympics ta birnin Los Angeles.

Ba kawai ta kasance mace ta farko da ta lashe tseren mita 400 ba, ta kasance mace ta farko 'yar Moroko da ta lashe lambar zinare a gasar Olympics a kasar, sannan wannan ne karon farko da aka gabatar da tseren yayin wasannin.

Mai yiwuwa ne wannan ne ya karfafa gwiwar abokin fafutukar Saïd Aouita wanda ya rubanya nasarar hau sau biyu kwanaki kadan baya, inda ya lashe gudun mita 500 na maza.

Abun da duniya za ta tuna a koda yaushe shi ne Nawal El Moutawakel ita ce mace Balarabiya ta farko da ta taba yin nasara a gasar Olympic.

A daren washe garin fafatawa ta karshe, El Moutawakel ta yi mafarke-mafarke game da tseren - da suka kunshi yadda ta dinga faduwa cikin rami bayan ta magance matsalarta.

"Tabbas na tsorata," El Moutawakel ta tunato.

"Ni kadai ce mace 'yar tsere a daukacin tawagar kasar Moroko, sannan kowa na yi min kyakkyawan fata.

"Ban iya yin bacci ba tsawon daren, ina tunanin tsere na, ina kallonta a cikin mafarkina, cikin mafarki na mai tsoratarwa, saboda jikina na bari, kuma na kasa kwanciya a gado sannan ina kallon kaina ina sassarfa."

'Wannan lokacinki ne'

Nawal El Moutawakel competing in the 1984 Olympics

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, El Moutawakel ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta lashe tseren mita 400 a gasar Olympics.

Ko da yake ba a sanya ta cikin wadanda aka yi zaton ba za su taka rawar a zo a gani ba, 'yar Morokon ta gamsu da kwazonta sannan ta himmatu domin tabuka abun a zo a gani yayin tseren.

"Na yi zaton zan kai ga mataki na karshe ne, kamar daya cikin takwas da za su rage a karshe, amma masu horas da ni suna karfafa min gwiwa kuma suna da kyakkyawan fata a kaina domin sun yi amannar zan yi nasara.

"Kafin fafatawa ta karshen, mun zauna tare da masu horas da mu sannan muka dinga kallon faya-fayen bidiyon tsere, ba don kawai mu more idanunmu ba amma mukan yi nazarin shahararru yan tsere irinsu Judi Brown, PT Usha dan kasar India, da Cojocaru daga Romania, sannan mukan yi nazarin nasarori da kuma gazawarsu.

"Sun ce dole in fara kuma in kai karshe da karfi na, domin zan iya yin nasara."

Yin amannar cewa za ta iya gabanin kammala tseren na da matukar muhimmanci ga nasarar El Moutawakel.

Ta kimtsa zuciyarta sannan ta mayar da hankalinta kan abu guda a halin yanzu: "Dole ki bar kasar nan da wani abu."

"Wannan shi ne lokacinki, wannan shi ne birnin, wannan shi ne lokacin, ba za ki rasa shi ba,"su ne abubuwan da ta dinga fadawa zuciyarta.

Tare da Ba'amurukiya - babbar kawarta, Judi Brown - a cikin tseren, filin wasan makere da 'yan kallon da ba sa goyon bayan 'yar tseren Morokon mai shekaru 22 da haihuwa. Yanayin ya yi kunci sannan kafafen yada labarai sun mayar da hankalinsu sosai.

A yunkurowar farko ta bazata - wadda El Moutawakel tun da fari ta yi tsammanin ya haifar mata da matsala- ya kara mata fargaba.

Bayan ta fahimci ba ita ce ta fara tashin farko ba, sai ta sake samun nutsuwa, sannan, a yunkuri na biyu, "ta yunkura kamar walkiya."

Ta kara da cewa "Na yi tsalle da kafar hagu a tsere na farko da biyu da na uku, sannan na ci gaba da sauyawa daga dama zuwa hagu har na kai karshe".

Ta tsunduma cikin tunani a kan kanta - har ta kai ga mamakin ko ita ce ta kuskure tashin farko ba tare da umarni ba kumamawa ba ta ji an sake kira ba.

"Na yi tunani - 'a in da sauran suke, me ya sanya ni kadai ce nake gudun?'"

"Amma a zahiri, na yi musu fintinkau. Sannan na fara waiwaye, kafin in kai karshe - na juya kaina, hagu da dama, domin in tabbatar ba ni kadai ce na faro gudun daga farko zuwa karshe ba. Ashe suna nan, dukkan sauran abokan tseren."

Lallai kam suna nan, - amma fa a can baya.

Lokacin murna da bakin ciki

Nawal El Moutawakel

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Nasarar El Moutawakel babban abun alfahari ga Moroko.

Duk da rage gudun da ta yi a karshen zangon tseren, Nawal El Moutawakel ta yi kokakari matuka inda ta kammala cikin dakikoki 54.61, kana Judi Brown ta lashe lambar azurfa cikin dakikoki 55.20.

Nasara ce mai ban mamaki ga Nawal El Moutawakel, kodayake ta hadu da bacin rai a karon farko domin babban mai goyon bayanta baya nan balle ya sheda.

Ta ce: "Na yi matukar farin ciki bayan na tsallake layin karshe - farin ciki na hakika - amma kuma na yi bakin ciki, saboda mahaifina, wanda shi ne mai karfafa min gwiwa na farko, ya rasu watanni kadan gabanin wannan tsere don haka bai iya shaida nasarar ta ba".

An haife ni cikin iyalin da suke son wasannan motsa jiki - mahaifinta dan wasan Judo ne sannan mahaifiyarta kuma yarwasan kwallon volleyball ce - iyayen El Moutawakel na karfafa mata gwiwar cimma burinta na zama shararriyar yarwasan motsa jiki a kowane lokaci. Dan haka ne aka tura ta Amurka domin cimma burinta kuma a lokaci guda ta yi karatu.

Amma sun yi tunanin tasirin da yar karamar yarinyar zata yi a duniya ta hanyar wasannin motsa jiki da kuma nasarorinta?

"Ga kasata, muhimmin al'amari ne da ba wanda yayi tsammani, matsahiya yar Moroko, mace da ta yi kokarin samun gurbi tsakanin shahararrun yanwasan motsa jiki kuma ba kawai ta samu gurbi ba ne har ta iya ciyo kyautar gwal sannan ta kawo shi gida … al'amari ne da zai zauna a zukatan al'umar Moroko" a cewar El Moutawakel.

"Lokaci mai dimbin tarihi da zai kasance a zukata kuma a zukata masu yawa."

Daga nan, babbar kofa mai fadin gaske ta bude ga dimbin 'yanmata matasa, ba kawai na Moroko ba har da sauran kasashen Larabawa da kuma Musulmai da a baya suke da tsauri sosai.

"Tun daga wannan lokacin, munga matan Moroko da yawa da suka zama zakaru a duniya - haka lamarin yake a kasashen Algeria daTunisia da Masar da kuma Bahrain," a cewarta.

"Kasashen da matansu ba sa halartar gasar wasannin Olympics. Bayan haka, ba kawai suna halarta ne ba, amma suna halarta ne domin su yi nasara ."