Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a fara cininkin 'yan kwallo a Premier da EFL tsakanin 27 ga Yuli
An tsayar da ranar 27 ga watan Yuli zuwa 10 ga watan Oktoba, domin bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a gasar Premier League da EFL, amma sai idan Fifa ta amince da hakan.
Haka kuma a kwai kasuwar cikin gida tsakanin Premier League da EFL da aka tsayar za ta ci daga 5 zuwa 16 ga watan Oktoba,
"A wannan lokacin kungiyoyin Premier za su ci kasuwa tsakaninsu da wanda ke gasa kasa da ta Premier League, ko dai a bayar da dan kwallo aro ko a saya gabaki daya'' in ji wata sanarwa daga Premier.
''Ba ciniki da za a yi tsakanin kungiyoyin Premier League a tsakanin a wannan lokacin''.
Hukumar da ke kula da kungiyoyin da ke buga gasar kasa da ta Premier League ta ce duk dan kwallon da ta saya a lokacin, ba zai buga wasa ba sai daga farkon kakar 2020-21.
''Wannan hukunci ya shafi kungiyoyin da za su buga wasannin cike gurbin shiga Premier League daga Championship.'' in ji sanarwar.
Za a rufe babbar kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ranar 5 ga watan Oktoba da karfe 11:00 na dare.
Ita kuwa wacce za a yi a cikin gida tsakanin kungiyoyin Premier League da na EPL za a rufe ranar Juma'a 16 ga watan da karfe 5:00 na yammaci.
Har yanzu ba a bayar da sanarwar ranar da za a fara kakar Premier League ta 2020-21 ba.
Wasu na cewa za a fara gasar Premier League ta badi daga ranar 12 ga watan Satumba, shi ma da zarar an kammala wasannin kasa da kasa da Fifa kan ware a watan na Satumba.