Chelsea ta kara kaka gida a mataki na uku bayan doke Norwich

Chelsea's Olivier Giroud scores in the first half

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Olivier Giroud ya ci kwallo da ka a karon farko a Premier tun bayan 24 ga watan Nuwamba a 3-1 da suka doke Tottenham
An wallafa

Chelsea ta kai kanta matakin samun gurbin shiga gasar Champions League ta badi, bayan da ta doke Norwich City 1-0 a Stamford Bridge.

Olivier Giroud ne ya ci kwallon da ka inda ta wuce mai tsaron raga, Tim Krul, bayan da Christian Pulisic ya kwaso mai ita.

'Yan wasan biyu sun kusan kara cin na biyu, sai dai Pulisic bai buga kwallo da karfin da zai kai wajen Giroud domin ya zura a raga ba.

Wannan nasarar na nufin Chelsea ta ci gaba da zama a matakinta na uku a kan teburi da tazarar maki hudu tsakaninta da Leicester City da Manchester United masu maki 59 iri daya.

Norwich City wacce za ta koma buga Championship a badi, bayan da West Ham ta dura mata 4-0, ta kasa kai hari ko sau daya a karawar da aka yi a Stamford Bridge.

Premier League table graphic

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Chelsea sit four points above Leicester City and Manchester United with two games remaining

Wannan nasarar da Chelsea ta yi zai kara mata kwarin gwiwa na buga wasan daf da karshe a FA Cup da Manchester United a Wembley ranar Lahadi.

Haka kuma Chelsea za ta ziyarci Liverpool wacce ta lashe kofin Premier League na bana, domin buga wasan mako na 37, sannan kwana hudu tsakani ta karbi bakuncin Wolverhampton a gida.

Daga nan ne Chelsea za ta buga gasar Champions League da Bayern Munich a Jamus a wasa na biyu na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar cikin watan Agusta.

A fafatawar farko da suka yi kan cutar korona ta kai tsako, Bayern ce ta yi nasarar doke Chelsea 3-0 a Stamford Bridge.