Liverpool na shirin tsawaita yarjejeniyar Lovren zuwa karshen 2022

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na shirya gabatar wa da mai tsaron baya, Dejan Lovren kunshin yarjejeniyar ci gaba da zama a Anfield zuwa karshen kakar 2022.
Kungiyar da ke buga gasar Rasha, Zenith St Petersburg na son yin zawarcin dan kwallon, amma har yanzu ba ta tuntubi Liverpool ba.
Mai shekara 31, ya koma taka leda a Liverpool daga Southampton kan fam miliyan 20 a Yulin 2014.
Lovren ya taimakawa Liverpool ta ci Premier League na bana, bayan da ya buga mata wasanni 10 a kakar shekarar nan.
Jumulla, Lovren ya yi wa Liverpool karawa 131 a Premier League ya ci kwallo biyar ya kuma lashe Champions League a 2019 da kungiyar ta Anfield ta dauka.
Zenith da wasu kungiyoyin na jan kafa cewar kwantiraginsa zai kare a Liverpool a karshen 2021, wanda hakan zai sa su dauki dan kwallo cikin sauki da arha.
Sai dai ba su kwan da sanin cewar cikin kunshin yarjejeniyarsa, Liverpool za ta iya tsawaita zamansa, kuma hakan zai sa mai tsaron bayan ya kara daraja a kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo.







