Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham ta hau kan Arsenal bayan cin 2-1 a Premier
Toby Alderweireld ne ya ci Arsenal kwallo na biyu, da ya bai wa Tottenham damar doke Arsenal a wasan hamayya na Arewacin Landan a gasar Premier League.
Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Alexandre Lacazette a minti na 16 da fara tamaula, sai dai minti uku tsakani Heung-min Son ya farke wa Tottenham.
Saura minti tara a tashi daga karawar Tottenham ta kara kwallo na biyu a raga ta hannun Toby Alderweireld.
Da wannan sakamakon, Arsenal wacce ke neman gurbin shiga gasar Europa League ta badi ta yi kasa zuwa mataki na tara da maki 50.
Ita kuwa Tottenham ta maye gurbin Arsenal ta koma ta takwas da maki 52, wato tazarar maki biyu kenan.
Ranar 15 ga watan Yuli, Arsenal za ta karbi bakuncin Liverpool wacce ta lashe kofin Premier League na bana tun saura wasa bakwai-bakwai.
Liverpool ce ta doke Arsenal 3-1 a wasan farko da suka fafata a Anfield ranar 24 ga watan Agustan 2019 a wasan mako na uku a gasar ta Premier League.
A ranar karawar Arsenal da Liverpool, ita kuwa Tottenham za ta ziyarci Newcastle United.