Sterling ya ci uku rigis a biyar da City ta doke Brighton

An wallafa

Raheem Sterling ne ya ci kwallo uku rigis a 5-0 da Manchester City ta shararawa Brighton a gasar Premier League ranar Asabar.

City ta sha kashi a wasa uku baya da ta yi a waje har da wanda Southampton ta doke ta ranar Lahadi, hakan ya sa kungiyar ta sa kwazo don kar ta kara jin kunya.

Sterling wanda ya hada kwallo 27 a dukkan wasannin da ya yi wa City a bana, shi ne ya addabi Brighton da sa kwazo har ya zura kwallo uku rigis a raga.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ingila shi ne ya ci West Ham United uku rigis da kuma Atalanta.

Sauran 'yan wasan da suka ci wa City kwallayen a karawar sun hada da Gebriel Jesus da kuma Bernardo Silva.

A wasan gabaki dayansa an fi karfin Brighton wacce ta yi ta kokarin kada kwallayen su yi mata yawa a raga.

City ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburin Premier League na bana, kuma ranar Litinin kungiyar ta Etihad za ta san makomarta a Champions League.

City ta daukka kara kan dakatar da ita kaka biyu da Uefa ta yi, bayan da ta sameta da laifin karya ka'ida ciki har da ta kashe kudi fiye da kima.