Makomar Sancho da Kepa da Havertz da Ronaldinho da Koulibaly da Rabiot

Asalin hoton, EPA
Borussia Dortmund tana cike da fatan dan wasanta mai shekara 20 dan Ingila Jadon Sancho zai ci gaba da murza leda a kulub din inda har yanzu babu wanda ya taya dan wasan.. (Sport Buzzer, via Goal).
Jurgen Klopp ya ce yana ganin Sancho ya fi dacewa da Liverpool amma ba tare da kocin ya ce zai dauko dan wasan ba a bana. (Bild, via Liverpool Echo)
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer bai yanke kauna ba kan Sancho idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a bazara. (Manchester Evening News)
Liverpool da ta lashe kofin Premier tana shirin taya dan wasan baya na Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29. (Tuttomercato, via Mail)
Chelsea na son dauko golan Ajax da Kamaru Andre Onana, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Kepa Arrizabalaga. Dan wasan na Sifaniya mai shekara 25 ana alakanta cewa zai koma Valencia. (Marca, via Express)
Kocin Bayer Leverkusen Peter Bosz ya amince Kai Havertz ya bar kulub din zuwa Agusta inda Chelsea da Real Madrid da Manchester United na cikin manyan kungiyoyin da ke son dauko dan wasan na Jamus mai shekara 21. (Sun)
Arsenal na son dan wasan tsakiya na Red Bull Salzburg dan HungarianDominik Szoboszlai. Tun 2019 ake cewa dan wasan mai shekara 19 ana cewa zai koma Arsenal. (Sun)
Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann na son karbar aiki a wata kasa idan kwangilar shi ta kawo karshe a 2023 - kuma kocin mai shekara 32 ana sa ran zai dawo Premier League. (Bild - in German)
Tsohon dan wasan Brazil Ronaldinho, mai shekara 40, yana son karba amsar gayyatar da Diego Maradona ya yi masa a kulub din Gimnasia idan ya fito daga daurin talala da ake masa a Paraguay. (Mundo Deportivo, via Sun)
Daraktan Juventus Fabio Paratici ya yi watsi da rade-radin dan wasan tsakiya Adrien Rabiot zai koma Manchester United ko Arsenal da Everton da ke son dan wasan mai shekara 24. (Sky Sports Italia, via Metro)
Musayar dan yan wasan da ake ta magana ta kusan tabbata inda Barcelona za ta bayar da dan wasanta na Brazil Arthur, mai shekara 23, Juventus kuma ta ba ta dan wasan Bosnian Miralem Pjanic, mai shekara 30, inda ake sa ran 'yan wasan biyu za a a diba lafiyarsu ranar Lahadi. (Calciomercato)
Real Valladolid ta tsawaita kwangilar Sandro Ramirez har zuwa karshen kaka amma ba ta cimma matsaya ba da Everton da ta ba ta aron dan wasan mai shekara 24. (Liverpool Echo)
Tottenham Hotspur za ta saurari wadanda ke bukatar taya dan wasanta na Ingila mai shekara 21 Kazaiah Sterling. (Football Insider)












