Callum Hudson-Odoi: Abin da ya sa aka daina bincikensa kan zargin fyade

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Alistair Magowan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Dan wasan Chelsea Callum Hudson-Odoi ya tabbatar cewa ba za a dauki karin mataki ba game da zargin da ake yi masa na aikata fyade.
An kama Hudson-Odoi, dan shekara 19, ranar 17 ga watan Mayu sannan aka bayar da belinsa.
Dan wasan na Ingila ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "A lokacin da duniya ke fama da manyan batutuwa yanzu, watakila kun lura da manyan zarge-zargen da ake yi a kaina.
"Na yi gum da bakina kuma na bai wa 'yan sanda hadin kai bisa dukkan tambayoyinsu, saboda ina sane cewa akwai ranar da za a wanke ni daga zarge-zargen.
"Bayan gudanar da cikakken bincike, yanzu 'yan sanda sun tabbatar mini cewa ba za su dauki karin mataki ba."
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar 'yan sandan birnin London ta ce: "An sallami mutumin da aka kama ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu bayan zarge-zargen yin fyade kuma ba za a dauki karin mataki a kansa ba.
"Don haka 'yan sanda sun daina gudanar da bincike kan wadannan zarge-zarge."
Chelsea ta ki cewa komai a kan batun.
Hudson-Odoi, wanda ya sabunta kwangilar shekara biyar da Chelsea a watan Satumba, shi ne dan wasan Premier na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar korona.
Sai dai ya warke sarai inda ya koma atisaye da abokan wasansa na Chelsea, kuma ranar 21 ga watan Yuni za su fafata da Aston Villa bayan dakatar da wasanni sakamakon cutar korona.











