Tomas Soucek zai ci gaba da zama a West Ham United

Asalin hoton, Getty Images
West Ham United ta tsawaita yarjejeniyar Tomas Soucek wanda ke buga mata wasannin aro har zuwa karshen kakar bana.
Dan wasan tawagar Jamhuriyar Czech ya koma West Ham buga wasannin aro a cikin watan Janairu daga Slavia Prague zuwa karshen kakar bana da ta kare a watan Mayu wadda cutar korona ta dakatar da wasanni.
Bayan da ake shirin ci gaba da gasar Premier an amince da doka cewar dun 'yan kwallon da kwantiraginsu zai kare zuwa karshen 30 ga watan Yuni za a iya sabunta ta idan yan wasa na taka rawar gani.
Soucer ya buga wa West Ham wasa hudu a fafatawar da ta yi da Brighton da Liverpool da Manchester City da kuma Arsenal.
Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier da wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield da na Manchester City da Arsenal.
Liverpool ce ke kan gaba a kan teburin gasar Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City.
West Ham tana mataki na 16 a kan teburin Premier da maki 27, bayan buga wasa 29 saura 11 suka rage mata a kakar bana.







