Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Coutinho na son komawa buga gasar Premier League'
Tsohon dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho na son komawa ci gaba da buga gasar Premier league in ji mai kula da harkokin wasanninsa, Kia Joorabchian.
Coutinho, mai shekara 27, ya koma Barcelona da taka leda daga Liverpool kan fam miliyan 142 a watan Janairun 2018, kan kwantiragin zuwa karshen kakar 2023.
Sai dai kuma Coutinho ya kasa taka rawar gani a Nou Camp, hakan ya sa Barcelona ta bayar da shi aro ga Bayern Munich a bara da yarjejeniyar sayar mata da shi idan ya sa kwazo.
Bayern Munich wadda ke mataki na daya a kan teburin Bundesliga da tazarar maki bakwai ba ta nuna aniyar sayen dan kwallon Brazil ba.
An yi ta alakanta cewar Coutinho zai koma Arsenal ko Chelsea ko Newcastle ko Tottenham da dai saura kungiyoyin da ke buga gasar Premier League.
Mai kula da harkokin wasannin dan kwallon tawagar Brazil, Joorabchian ya ce Coutinho yana matukar son ya koma ci gaba da taka leda a gasar Premier League.
Za a ci gaba da wasannin gasar bana ranar 17 ga watan Yuni da kwantan wasa biyu tsakanin Aston Villa da Shieffield United da karawa tsakanin Arsenal da Manchester City.
Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a Ingila don gudun yada cutar korona.