Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyoyin da ke buga Serie A za su koma yin atisaye a watan Mayu
'Yan wasan da ke buga Serie A za su fara atisaye ranar 4 ga watan Mayu, sannan kungiyoyi su fara 18 ga watan a kokarin da Italiya ke yi na cire dokar hana fita.
Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar Serie A tsakanin 27 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni, inda ake sa ran karkare kakar 2019-20 cikin watan Agusta.
An samu rahoton mutuwar mutum 26,644 da cutar korona ta hallaka a Italiya - kasar da annobar ta dauki ran mutane da dama fiye da kowacce kasa a Turai.
A ranar Lahadi mutum 260 ne suka mutu, ita ce ranar da aka samu karancin mace-mace a kasar tun daga 14 ga watan Maris.
Firai Minista, Giuseppe Conte ya fada cewar 'yan wasa za su fara atisaye daga 4 ga watan Mayu, sannan su yi a cikin rukuni tare da kungiyoyi daga 18 ga watan.
Hukumar kwallon kafar Italiya na fatan fara gwajin 'yan kwallo daga farkon watan Mayu, domin kauce wa yada cutar korona tsakanin 'yan wasa.
A ranar 9 ga watan Maris aka dakatar da wasannin Serie A, bayan da 'yan wasa da dama suka kamu da cutar korona.
Saura wasanni 12 suka rage da kwantan wasa hudu a karkare kakar bana, inda Juventus ke gaba a teburin gasar da tazarar maki daya tsakaninta da Lazio ta biyu.