Coronavirus: Wasannin da aka yi a watan Maris suka kara rura annobar

Asalin hoton, European Photopress Agency
Manyan wasanni biyu da aka yi a cikin watan Maris a Burtaniya ne suka kara rura yaduwar cutar korona in ji farfesa Tim Spector.
Wasu bincike da aka yi na tara bayanai daga 'yan sa kai mutum sama da miliyan an tabbatar cewar an yada annobar da yawa a lokacin bikin Cheltenham da wasan Liverpool da Atletico Madid a gasar Champions League.
Kasa da wata uku da suka wuce an ci gaba da wasanni a Burtaniya kamar yadda aka saba duk da an samu labarin bullar cutar korona, bayan da wasu kan yi wasanni a Turai ba 'yan kallo ko kuma sun dage su.
Kuma tun cikin watan Maris, Firai minista, Boris Johnson ya umarci mutane da kowa ya ci gaba da sabgogi kamar yadda aka saba.
A makon farko a watan Maris an ci gaba da wasannin Premier kamar yadda aka saba da sauran wasannin makon, inda a Scotland aka yi gasar sukuwar dawakai biyar da wasan zari ruga tsakanin Ingila da Wales, kuma Firai minista ya halarci wasan a Twickenham .
Yayin da a lokacin aka soke gasar zari ruga a Dublin da tseren Formula 1 ta Chinese Grand Prix da wasu wasannin tamaula da aka yi ba 'yan kallo a Italiya.
Daga ranar 10 ga watan Maris aka fara gasar tseren dawakai ta Cheltenham wadda aka yi kwana uku da mutum 250,000 suka halarta duk da labarin bullar cutar korona.

Asalin hoton, European Photopress Agency
Haka kuma a cikin watan Maris Liverpool ta karbi bakuncin Atletico Madrid a gasar Champions League da suka kara a Anfield.
Kuma kimanin magoya baya 3,000 ne daga Spaniya suka je Merseyside inda suka yi hulda da mutane a wajen cin abinci da sauransu, wanda a lokacin Spaniya tana daga cikin kasashen da annobar ta yadu da yawa, inda kusan rabin mutanen kasar ke dauke da ita.











