An bayar da belin Callum Hudson-Odoi dan Chelsea bayan da aka tsare shi

Asalin hoton, Getty Images
An bayar da belin dan wasan tawagar kwallon kafa ta Ingila mai wasa a Chelsea, Callum Hudson-Odoi bayan da aka tsare shi a sanyin safiyar Lahadi.
Hakan ya biyo bayan wani rahoto da jami'an tsaro suka samu kan wata mata mara lafiya.
An kira motar asibiti zuwa adireshin da ke Kudu maso yamma da Landan, inda aka dauki matar aka garzaya da ita asibiti.
An kama Hudson-Odoi, mai shekara 19 a wurin da lamarin ya faru. An bayar da shi beli zai koma wajen 'yan Sanda cikin watan Yuni don ci gaba da bincike.
Chelsea ba ta ce komai ba kan wannan batun.
Hudson-Odoi, wanda ya buga wa tawagar Ingila wasa uku, ya zama na farko da aka samu da cutar korona a cikin watan Maris.
Daga baya dan kwallon ya warke sarai, kuma yan wasan Chelsea na shirin fara atisaye a kokarin da ake yi na ci gaba da gasar Premier ta bana.











