Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Ingila sun bai wa jami'an lafiya gudunmawa
'Yan wasan da ke yi wa Ingila sun bayar da gudunmawa ga jami'an lafiya da ke kula da masu fama cutar korona.
Sun bayar da taimakon kudi ne na ladan wasa tun daga watan Satumbar 2018.
A watan jiya ne tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta sanar cewar za ta bai wa ma'aikantan lafiya gudunmawa kudi.
Haka ma 'yan kwallon tawagar Scotland maza da na mata sun bi sahun na Ingila inda jumulla suka bayar da gudunmawar kudi ga jami'an lafiyar.
A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Ingila.
Liverpool wadda rabon ta da kofin Premier tun shekara 30 tana mataki na daya a kan teburin bana da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City.