Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Loris Karius: Golan Liverpool ya soke kwantiraginsa a Besiktas
Golan Liverpool, Loris Karius ya ce ya soke kwantiragin kaka biyu da yake buga wasannin aro a kungiyar Besiktas ta Turkiya.
Mai shekara 26 yana cikin kaka ta biyu da yake buga wasannin aro a Istanbul, ya kuma buga wasa 30 kafin a dakatar da karawar bana saboda tsoron yada cutar korona.
Karius ya fada a shafinsa na sada zumunta a Instagram cewar ''Abin kunya ne da suka raba gari ta wannan hanyar.
Dan kasar Jamus ya kara da cewar ''Na yi hakuri sosai, na dade ina ta magana da mahukuntan kungiyar amma abin da ya faru a bara dai shi ne''.
A makon jiya dan kasar Jamus ya kai karar Besiktas ga hukumar kwallon kafar duniya, Fifa kan rashin biyansa albashi karo na biyu, daga baya suka amince za su cimma matsaya ba tare da sa hannun Fifa ba.
Bayan da Karius ya soke kwantiraginsa da Besiktas, kungiyar za ta biya shi fam 400,000 da yake binta.
Karius wanda ya yi wa Liverpool wasan karshe, bayan nasarar da Real Madrid ta yi a Champions League a 2018 ya ce Besiktas sunki yadda da shawarar da ya ba su cewar su rage masa albashi.