Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham za ta dauko Rakitic, Inter Milan tana zawarcin Pogba
Tottenham tana kan gaban sauran kungiyoyin da ke son dauko dan wasan Barcelona da Croatia, mai shekara 32, Ivan Rakitic, a cewar jaridar (Mundo Deportivo - in Spanish).
Inter Milan tana son dauko dan wasan Manchester United da Faransa, Paul Pogba, mai shekara 27. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Jaridar Telegraph ta rawaito cewa dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23, yana son ci gaba da zama sannan ya fafata don samun gurbi a Tottenham a yayin da ake rade radin cewa Barcelona za ta dauko shi.
Roma da Real Betis suna zawarcin dan wasan Chelsea da Spaniya, Pedro, mai shekara 32. (Goal)
Jaridar (Mirror ta ce Arsenal ta shirya sayar da dan wasan Armenia Henrikh Mkhitaryan a bazara domin ta tara kudi. Dan wasan tsakiyar mai shekara 31 yana Roma inda yake zaman aro.
Sevilla tana sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Faransa Tiemoue Bakayoko. Dan wasan mai shekara 25 yana Monaco inda yake zaman aro daga Chelsea.(France Football - in French)
Arsenal da Chelsea suna son sayo dan wasan Turkiyya Feyenoord Orkun Kokcu, mai shekara 19 (Express)
Dan wasan Real Madrid da Spaniya Lucas Vazquez, mai shekara 28, ya ce tsarin buga tamaula a kulob-kulob da ake yi a Ingila "yana matukar jan hankalinsa". (Guardian)
Manchester United ta tuntubi wakilan dan wasan RB Leipzig dan kasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 20. (Le10 Sport - in French)
Shahararren dan wasan Manchester United da Netherlands Jaap Stam, mai shekara 47, ya ce ya tattauna da FC Cincinnati da zummar kasancewa sabon kocin kungiyar MLS. (Goal)