Liverpool za ta dauko Werner da Wilian, Sancho ba zai bar Borussia Dortmund ba

An wallafa

Dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 24, ya shirya komawa Liverpool idan kungiyar za ta biya shi £52m. (Sky Sports)

Shi ma dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, yana tattaunawa da Liverpool domin komawa kungiyar idan kwangilarsa ta kare. (Sport - via Mirror)

Borussia Dortmund za ta cika jakar Jadon Sancho, mai shekara 20, da kudin da zai sa ya zama na biyu a jerin 'yan wasan da suka fi daukar albashi a kungiyar don hana Manchester United da Chelsea dauke shi. (Forbes)

Manchester United na shirin sayar wa Paris St-Germain dan wasan Portugal Diogo Dalot, mai shekara 21. (Daily Mercato)

Philippe Coutinho zai iya koma ganiyarsa idan dan wasan na Brazil mai shekara 27 ya bar Barcelona zuwa Chelsea, a cewar shahararren dan wasan Brazil Rivaldo. (Sun)

Liverpool ta shaida wa Coutinho cewa ba za su sayo shi daga Barcelona ba. (Sport Witness)

Tsohon dan wasan Liverpool da Chelsea Glen Johnson ya bai wa Chelsea shawarar dauko Coutinho. (Talksport - via Express)

Leicester City ta shirya yin gogayya da Manchester United a yunkurin sayo dan wasan Borussia Monchengladbach da Faransa Alassane Pea, mai shekara 27. (Le10 Sport - via Leicester Mercury)

Dan wasan Aston Villa Jack Grealish zai zama dan wasan gaba a Manchester United idan kungiyar ta kammala sayen dan kasar ta Ingila mai shekara 24. (Athletic - vial Birmingham Mail)

Juventus na duba yiwuwar dauko dan wasan Napoli da Poland Arkadiusz Milik, mai shekara 26 a bazara. (Calcio Mercato)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya samu kwarin gwiwar sayo dan wasan Feyenoord Orkun Kokcu, mai shekara 19, a yayin da kungiyar ta shirya domin sayar da wasu 'yan wasanta domin dauko babban dan wasa a bazara (Voetbal International - via Express)

Dan wasan Arsenal dan kasar Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31, yana fatan ci gaba da zama a Italiya a kungiyar Roma a kakar wasa mai zuwa a matsayin aro, yayin da kungiyar ta sanya dan wasan Manchester United da Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, cikin shirinta na musayar 'yan kwallo bayan ya yi rawar gani a zaman aron da ya yi a can. (Mail)

Arsenal na shirin kammala sayen dan wasan Flamengo dan kasar Spaniya Pablo Mari, mai 26, wanda ya koma Arsenal a watan Janairu a matsayin aro. (Athletic)

Jamie Carragher ya ce 'yan wasan Liverpool sun yi matukar 'kaduwa' game da yadda kungiyar ta sayar wa Chelsea Fernando Torres a kan £50m a 2011. (Sky Sports - via Mail)

Juventus tana neman kungiyar da za ta sayi dan wasan Italiya Federico Bernardeschi, mai shekara 26 (Goal - in Italian)