Za a rage wa 'yan wasan Arsenal albashi

An wallafa

'Yan wasan Arsenal za su kasance 'yan wasan wata kungiyar Premier na farko da za su amince a rage musu albashi bayan da aka ba su gurbin shiga gasar Champions League.

Yanzu za a yanke wa 'yan wasan na Arsenal kashi 12.5 to amma za a mayar musu da abin da aka yanke musu idan sun samu gurbin shiga gasar Champions League.

'Yan wasan za su samu kyautar kudi fan 100,000 idan suka shiga gasar ta Champions League ta bana.

Kowanne a cikinsu zai karbi fan 500,000 idan suka yi nasarar cin Champions League ta 2021 ko kuma fan 100,000 idan suka samu nasara a gasar Europa League.

Arsenal ce dai mai matsayi na tara a teburin gasar Premier lokacin da aka dakatar da gasar sakamakon bullar annobar korona.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugabannin kulob din suka amince a rage fiye da kaso daya cikin uku na albashinsu a tsawon watanni 12 masu zuwa.