Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United tana son dauko Coutinho, za a sayar da Pogba a kan £100m
Manchester United ta nemi sayo dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, daga Barcelona. (Mundo Deportivo)
United za ta amince a biya ta £100m a kan dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27. Real Madrid da Juventus na son sayo dan wasan. (Sun)
Chelsea na son dauko dan wasan Arsenal Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30. (90min)
Atletico Madrid na duba yiwuwar tsawaita zaman dan wasan Ghana Thomas Partey, mai shekara 26, zuwa 2025 kuma za ta rka biyansa €100m a yayin da ake rade radin cewa Arsenal da Manchester United suna zawarcinsa (Goal)
Dan wasan Bosnia Miralem Pjanic, mai shekara 29, zai iya barin Juventus a bazara, a yayin da ake hasashen cewa Manchester City da Chelsea suna son daukarsa. (Corriere dello Sport via Sport Witness)
Dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, ya ce zai ci gaba da murza wa kungiyar kwallo zuwa karshen kakar wasa ta bana, ko da kuwa hakan ya zarta wa'adin kwangilarsa (Star)
Dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, na cikin 'yan wasan da Everton ke son daukowa a bazara. (Liverpool Echo)
Golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 21, zai bar AC Milan inda zai koma Paris St-Germain ko kuma wata kungiyar da ke buga gasar Firimiya. . (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Inter Milan sun gaya wa Barcelona cewa suna son kulla yarjejeniyar da za ta kai ga ba su zunzurutun kudi ne kawai a kan dan wasan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22 (Sport - in Spanish)
Dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 27, na duba yiwuwar barin Bayern Munich inda ake sa ran zai koma Real Madrid ko Barcelona. (Sport Bild - in German)
Manchester United na duba yiwuwar sake dauko tsohon dan wasansu Eric Cantona, mai shekara 53, domin ba shi mukamin wakilin kungiyar. (Mirror)