An fitar da Real Madrid a Copa del Rey na bana

An wallafa

Real Madrid ta yi ban kwana da Copa del Rey na bana, bayan da Real Sociedad ta doke ta 4-3 a Santiago Bernabeu ranar Alhamis

Real Sociedad ta fara cin kwallo ta hannun Martin Odegaard minti 22 da fara tamaula a karawar daf da na kusa da na karshe.

Bayan da aka koma hutu ne Alexander Isak ya kara ci wa Sociedad na biyu, kuma minti biyu tsakani ya kara na uku.

Daga nan ne Real ta zare kwallo daya ta hannun Marcelo Vieira Da Silva, amma kuma Mikel Merino ya ci wa Sociedad na hudu

Koda yake Real ta kara rage kwallo ta hannun Rodrygo da kuma wadda Nacho Fernandez ya ci mata.

Real Sociedad ta karasa fafatawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Andoni Gorosabel jan kati.

An kuma kawo karshen wasa 21 da Real ta yi a jere ba tare da an doke ta ba a bana.

Rabon da Real Madrid ta lashe Copa del Rey tun na kakar 2013/14, kuma ita ce ta uku a yawan lashe kofin da take da 19.

Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai guda 30, sai Atletico Bilbao mai 23.

Valencia ce mai rike da kofin, wadda Granada ta fitar da ita ranar Talata da ci 2-1.

Real Madrid za ta mai da hankali a gasar La Liga da za ta buga wasan mako na 23 da za ta ziyarci Osasuna ranar Lahadi.

Real tana ta daya a kan teburin La Liga, yayin da Barcelona ke biye da ita.

Rabon da a ci Real Madrid tun 1-0 Mallorca ta yi nasara ranar 19 ga watan Oktoba a gasar La Liga.