Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwallo 13 ne a ragar Real Madrid a La Liga
Real Madrid ta zama kan gaba a manyan gasar Turai da ba a zura mata kwallaye da yawa ba a raga a La Ligar bana.
Kwallo 13 ne kawo yanzu suka shiga ragar Real, karkashin jagorancin Zinedine Zidane.
Babu wata kungiyar da ke gasar Spaniya ko Ingila ko Italiya ko Jamus ko kuma Faransa da ba a zura wa kwallo ba fiye da na Real.
Wadan da ke biye da ita sun hada da Atletico Madrid da Paris St Germain da Stade Reims da aka ci kwallo 14 a raga.
A Ingila kuwa Liverpool ce mai karfin masu tsaron baya, yayin da kwallo 15 ne suka shiga ragarta a gasar Premier.
Wannan kokarin da kwallo 13 suka shiga ragar Real, bayan buga wasannin mako na 21 a La Liga ya sa ta yi kan-kan-kan da bajintar da ta yi a 1964/65 da kuma 1987/88.