Plateau United ta dare teburin Firimiyar Najeriya

Nigerian Premier League

Asalin hoton, NPFL

An wallafa

Kungiyar Plateau United ta hau kan teburin Firimiyar Najeriya, bayan da ta yi nasara a kan Rivers United a ranar Lahadi.

Plateau wadda ta karbi bakuncin Rivers ta ci kwallon ne ta hannun Ibrahim Mustapha minti uku da fara wasan mako na 18 da suka fafata.

Da wannan sakamakon Plateau wadda ta yi wasa 18 ta hada maki 32 kenan, ita kuwa Lobi Stars mai kwantan wasa rashin nasara ta yi da ci 1-0 a hannun Jigawa Golden Stars.

Hakan ne ya sa Jigawa ta bar 'yan kasan teburi ta koma ta 16 da maki 17 da kwantan wasa daya.

Shi kuwa karawa tsakanin Warri Wolves da Enyimba dana Enugu Rangers da Katsina United ba a yi shi ba.

Rangers da Enyimba na buga gasar kofin Zakarun Afirka na Confederation.

Sakamakon wasannin mako na 18

  • Jigawa GS 1-0 Lobi
  • FC Ifeanyiubah 0-0 Akwa United
  • Heartland 1-0 Sunshine Stars
  • Kano Pillars 2-0 Adamawa United
  • Kwara United 1-0 MFM
  • Plateau United 1-0 Rivers United
  • Wikki 1-1 Dakkada
  • Nasarawa United 3-1 Abia Warriors

Za a buga wasannin mako na 19

Lahadi 9 ga watan Fabrairu 2020

  • Enyimba da Abia Warriors
  • Lobi Stars da Wikki Tourists
  • Sunshine Stars da Ifeanyi Ubah
  • Adamawa United da Heartland
  • Akwa United da Enugu Rangers
  • Jigawa Golden Stars da Nasarawa United
  • Katsina United da Warri Wolves
  • Mountain Of Fire And Miracles da Kano Pillars FC
  • Rivers United da Kada City
  • Akwa Starlets da Plateau United