Real Madrid ta yi wasa 21 a jere ba a doke ta ba

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Asabar Real Madrid ta doke Athletico Madrid da ci 1-0 a wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu.
Wasan kuma shi ne na 21 da Real Madrid ta kara a jere ba tare da an doke ta ba, guda shida daga ciki canjaras ta tashi.
Rabon da a doke Real tun rashin nasara da ta yi da ci 1-0 a gidan Mallorca a gasar La Liga da suka fafata ranar 19 ga watan Oktoba.
Cikin wadan da Real ta doke har da Galatasaray gida da waje a gasar Champions League da doke Club Brugge 3-1, bayan da ta yi 2-2 da Paris St Germain.
Real din ta doke Atletico Madrid karo biyu kenan, bayan a Spanish Super Cup da suka tashi 0-0, kungiyar ta Santiago Bernabeu ta lashe kofin a bugun fenariti.
Sauran kungiyoyin da Real ta doke sun hada da Leganes da Real Betis da Eibar da Real Sociedad da Alaves da Espanyol da Valencia da Getafe da Sevilla da kuma Valladolid duk a gasar La Liga.
Haka kuma Real ta ci Unionistasda kuma Real Zaragoza a Copa del Rey, inda hakan ya sa ta kai matakin daf da na kusa da na karshe.
Wasannin da Real za ta yi a cikin watan nan na Fabrairu
Gasar La Liga 9 ga watan Fabrairu za ta je Osasuna
Gasar La Liga 16 ga watan Fabrairu za ta karbi bakuncin Celta Vigo
Gasar La Liga 22 ga watan Fabrairu za ta je Levante
Gasar Zakarun Turai 26 ga Fabrairu za ta karbi bakuncin Manchester City
Real Madrid tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 49, bayan buga wasannin mako na 22.
Barcelona wadda ta yi karawa 21 tana biye da Madrid da maki 43.











