Real Madrid ta dare kan teburin La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La liga, bayan buga fafatawar sati na 21 a karshen mako.

Real ta samu wannan damar ce, bayan da ta ci Real Valladolid 1-0, kuma Nacho Fernandez ne ya ci mata kwallon.

Hakan ne ya sa Real ta hada maki 46 kenan, bayan cin karawa 13 da canjaras bakwai da rashin nasara daya.

Kungiyar ta Santiago Bernabeu ta kuma ci kwallo 39, sannan aka zura mata 13, bayan kammala wasannin mako na 21 a La L;iga.

Ita kuwa Barcelona wadda ta dawo ta biyu da maki 43 ta ci karo da koma baya ne, bayan da Valencia ta yi nasarar doke ta 2-0.

Za a ci gaba da wasannin mako na 22 ranar Juma'a 31 ga watan Janairu, inda za a kece raini tsakanin Villarreal da Osasuna.

Kawo yanzu Lionel Messi na Barcelona ne kan gaba a cin kwallo a gasar ta La Liga da guda 14 a raga.

Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ne ke biye da shi da kwallo 12 a raga.

Wasannin mako na 22 a gasar La Liga.

Juma'a 31 ga watan Janairu

  • Villarreal da Osasuna

Asabar 1 ga watan Fabrairu

  • Granada da Espanyol
  • Real Madrid da Atletico de Madrid
  • Real Mallorca da Real Valladolid
  • Valencia da Celta de Vigo

Lahadi 2 ga watan Fabrairu

  • Leganes da Real Sociedad
  • Eibar da Real Betis
  • Athletic Bilbao da Getafe
  • Sevilla da Deportivo Alaves
  • Barcelona da Levante

Wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga:

  • Lionel Messi Barcelona 14
  • Karim Benzema Real Madrid 12
  • Luis Suarez Barcelona 11
  • Angel Getafe 9
  • Chimy Avila Osasuna 9
  • Roger Marti Salvador Levante 9
  • Lucas Perez Martinez Deportivo Alaves 8
  • Gerard Moreno Villarreal 8
  • Maximiliano Gomez Valencia 8
  • Loren Moron Real Betis 8
  • Willian Jose Real Sociedad 8
  • Ante Budimir Real Mallorca 8