La Liga: Valencia ta cinye Barcelona

Maxi Gomez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maxi Gomez ne ya zira wa Barca kwallo har biyu
An wallafa

Valencia ta lallasa Barcelona da ci 2-0 a wasan La Liga mako na 21 a filin wasa na Estadio de Mastella da ke Valencia a karon farko tun shekarar 2007.

Kashin farko kenan da sabon mai horarwa Quique Setien ya sha, wanda tawagarsa ta rike kwallo a mafi yawan wasan, inda Messi shi kadai ya buga shot 11 - 4 daga ciki na-ci ne.

Tun a minti na 11 da fara wasa Valencia ta samu finareti bayan Gerrard Pique ya kayar da Jose Gaya a cikin yadi na 18. Sai dai Ter Stegen ya kade kwallon da Maxi Gomez ya buga.

A minti na 48 ne kuma Gomez din ya ci kwallon farko bayan ya shaka wata kwallo ta daki jikin Jordi Alba ta fada raga.

Barca ta so ta farke bayan wani ba-ni-in-ba-ka tsakanin Lionel Messi da Ansu Fati amma Fati bai iya saka ta a raga ba, inda kwallo ta yi fadi.

Saura minti 13 wasa ya kare kuma Gomez ya samu kwallo a bangaren hagu, inda ya natsu ya take ta kuma ya lafa ta a ragar Stegen, wanda ya kame a tsaye ba tare da wani yunkuri ba.

Sakamakon ya sa Barca ta dawo maki daya da Real Madrid, wadda za ta buga wasanta da Real Valladolid a gobe Lahadi.

Idan Real din ta ci za ta haye saman Barca da maki uku.

Teburin La Liga