Inter na fatan daukar Eriksen nan da Litinin

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan tana fatan kammala daukar Christian Eriksen daga kungiyar Tottenham zuwa nan da ranar Litinin.
Dan kasar Denmnark din bai san makomarsa ba tun daga karshen kakar bara lokacin da ya ce a shirye yake ya koma buga wata gasar daban ba Premier Ingila ba.
Bayan yunkurinsa na komawa kasar Sifaniya ya ci tura a farkon kakar bana ne kuma ya ci gaba da wasa da Tottenham din.
Akwai alamar cewa an cimma wata yarjejeniya a kan dan wasan mai shekara 27, wadda kuma za a kammala ta a mako mai zuwa.
Eriksen wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana a Tottenham, ana sa ran zai kai fan miliyan 16, duk da irin rashin kokarin da yake yi a yanzu.
Babu sunan dan wasan tsakiyar a tawagar da za ta fafata da Southampton a wasan FA a yau Asabar.
Zai zama dan wasa na uku da zai koma Inter Milan a watan Janairu daga Premier Ingila, bayan Ashley Young - daga Manchester United - da Victor Moses - a matsayin aro daga Chelsea.
Inter na matsayi na biyu a teburi da tazarar maki hudu tskaninta da Juventus wadda ke saman teburin.











