Man Utd. na iya dawo da Carlos Tevez, Liverpool na son raba Isco da Madrid

Carlos Tevez playing for Boca Juniors

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A wani yunkuri na ba zata, Manchester United na iya dawo da dan wasan gaba na Argentina Carlos Tevez mai shekara 35. (Tuttosport)

Tottenham Hotspur ta amince ta kulla yarjejeniyar euro miliyan 20, kimanin fiye da fam miliyan 16 da Inter Milanto, kan sayar da dan wasanta na tsakiya Christian Eriksen mai shekara 27. (Sempreinter.com)

Sai dai, Barcelona ta fara neman dan wasan Denmark din Eriksen a wannan watan. (Sky Sports)

Liverpool na nuna sha'awar daukar dan wasan tsakiyar Real Madrid Isco dan shekara 27, sai dai babbar kungiyar ta La Liga na son kimanin euro miliyan 70 don sayen dan wasan. (El Desmarque - in Spanish)

Mundo Deportivo ta ruwaito cewa kofar dan wasa Pierre-Emerick na Arsenal mai shekara 30 a bude take ya koma Barcelona.

A hannu guda kuma, Gunners na nuna sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Faransa, Thomas Lemar dan shekara 24 daga Atletico Madrid. (Express)

Chelsea ta sake komawa teburin tattaunawa da Lyon kan yarjejeniyar daukar dan wasa Moussa Dembele mai shekara 23, a wannan watan ko da sun rasa damar sayen dan wasan PDG Edinson Cavani mai shekara 32. (Sun)

Manchester United na duba yiyuwar neman dan wasan gaban Uruguay, Cavani, cikin wannan makon. (Telegraph)

Yunkurin Manchester United na neman Bruno Fernandes ya lafa saboda gaza biyan kudin da Sporting Lisbon ta saka na fam miliyan 68, idan har suna son sayen dan wasan tsakiyar Portugal din mai shekara 25. (Mail)

United na ci gaba da kwadayin sayen dan wasan tsakiya na Leicester City James Maddison, mai shekara 23. (Star)

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Southampton dan shekara 24, Pierre-Emile Hojbjerg shi ne babban zabin kocin Everton Carlo Ancelotti. (Star)

Chelsea kuwa na dab da rasa damar samun sayen dan wasan Spaniya kuma mai bugawa Dynamo Zagreb, Dani Olmo mai shekara 21. (Express)

Blues din da Barcelona na zawarcin dan wasan Grasshopper Alan Arigoni mai shekara 21. (Blick - in German)