NPFL: An ci tarar Pillars da Katsina United

An wallafa

Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya League Management Company (LMC), ta ci tarar kungiyoyin Kano Pillars da kuma babbar abokiyar hamayyarta Katsina United tarar milyan ₦4.7.

Wannan tara ta biyo bayan rashin da'a da magoya bayan kungiyoyin suka nuna a wasan mako na 15 da aka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.

Katsina United za ta biya tarar miliyan ₦3.5, ita kuma Pillars za ta biya milyan ₦1.2 sannan kuma za su biya wasu kudin na gyaran filin wasan Muhammadu Dikko da magoya bayansu suka bata yayin wasan.

Kazalika wasannin gaba da za ku buga ba za su yi shi ba tare da 'yan kallo ba "har sai sun zauna tare sun magance kaifin hamayyar da ke tsakaninsu," in ji LMC.

Har wa yau, Katsina United za ta ci gaba da yin wasanninta na gida ba tare da magoya bayanta sun shiga kallon wasannin ba.

Laifukan da magoya bayan Katsina United suka aikata na jefa abubuwa cikin fili kan 'yan wasan Pillars ya saba da sashe na B13.18 da kuma ka'idar C19 na kundin dokar hukumar, abin da ya sa 'yan wasa da kuma allkalan wasan suka kasa fita daga fili yayin hutun rabin lokaci.

Su ma magoya bayan Pillars sun mayar wa da 'yan Katsina martani, abin da ya saba wa ka'idar sashen dokar C1 mai hukuncin B15.17, in ji LMC.

Kano Pillars tana matsayi na 12 a teburin Firimiyar da maki 20 kuma a kasan Katisina United a mataki na 11 da makinta 21.