Liverpool ta ki sallama tayin Xherdan Shaqiri

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Liverpool ta ki sallama tayin da Roma da Sevilla suka yi wa Xherdan Shaqiri, domin ya buga musa wasannin aro.
Kungiyar ta Anfield ba ta shirya rabuwa da Shaqiri a Janairun nan ba, bayan da ta ke shirin lashe Premier League tana kuma buga Champions League da FA Cup.
Liverpool ba ta yadda ta bayar da Shaqiri, mai shekara 28, don ya buga wasan aro ko kuma a saye shi gaba daya ba.
Liverpool ba za ta sayar da dan wasan na tawagar Switzerland ba har sai karshen kakar bana, lokacin darajarsa ta kai fam miliyan 25.5.
Kungiyar ta Anfield ta dauko Shaqiri daga Stoke City a watan Yulin 2018, bayan da ta biya kunshin yarjejeniyarsa ta fam miliyan 13.






