Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Henderson ne gwarzon dan kwallon Ingila a 2019
An bayyana Jordan Henderson a matsayin gwarzon dan wasan Ingila a shekara ta 2019.
Haka kuma Lucy Bronze ce macen da babu kamarta a fagen tamaula a shekarar da muka yi ban kwana da ita.
Kyaftin din Liverpool, mai shekara 29, ya yi takara ne da Raheem Sterling da kuma Harry Kane.
Ita kuwa Bronze mai wasa a kungiyar kwallon kafa ta mata ta Lyon, ta yi nasara ne a kan Ellen White da kuma Beth Mead.
Bronze mai tsaron baya ta taimakawa tawagar mata ta Ingila lashe SheBelieves Cup a karon farko da kai wa wasan daf da karshe a kofin duniya.
'Yar kwallon wadda ta buga wa Ingila wasa 81, ita ce ta lashe kyautar fitatciyar 'yar wasan Turai a 2019, bayan da Lyon ta ci kofi.
Henderson, wanda ya buga wa Ingila wasa na 50 a watan Maris ya bayar da gudunmawar da Ingila ta kai gasar Euro 2020 da kai wa mataki na uku a Uefa Nations League.
Dukkansu 'yan wasan biyu sun ci wa kungiyoyinsu Champions League.