Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AC Milan za ta dauki gola, Asmir Begovic
AC Milan ta aunar koshin lafiyar golan Bournemouth, Asmir Begovic, a shirin daukarsa aro zuwa karshen kakar bana.
Milan na neman mai tsaron raga ruwa a jallo, bayan da ta amince Pepe Reina ya je Aston Villa da zai yi wasa aro zuwa karshen kakar da muke ciki.
Begovic, mai shekara 32, ya buga wa Bournemouth wasa 62, tun komawarsa can da taka leda daga Chelsea a shekarar 2017.
Dan kasar Bosnia ya rasa gubinsa, inda bai buga wasa akai-akai, dalilin da ya sa aka bayar da aronsa ga Qarabag ta Azerbaijan.
Bournemouth na amfani da Aaron Ramsdale a matsayin mai tsaron raga, yayin da Mark Travers ke yin mataimaki.