Tottenham: Harry Kane zai yi jinyar makonni

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban kasar Ingila da kuma Tottenham Harry Kane ya ji rauni a bayan kokon gwaiwarsa, kamar yadda kungiyarsa ta bayyana.
Dan wasan ya fita daga fili da dingishi a wasan da Southampton ta doke su da 1-0 a ranar Laraba sannan ranar Juma'a Jose Mourinho ya ce yana jiran ya ji "labari maras dadin ji".
Zuwa yanzu ba a bayyana tsawon lokacin da zai dauka ba amma da alama ba zai buga wasanni ba na wasu makonni, ciki har da wasan FA Cup a Middlesbrough ranar Lahadi.
"Wuya ba ta kisa, jajirtattu ne suke yi", Kane ya wallafa a shafinsa na Twitter.
"Kowa ya san wane ne shi, amfaninsa ga tawagarmu da kuma magoya baya," in ji Mourinho.
"Kwarewarsa da karsashin da kungiyar take samu idan yana wasa, duk za mu yi kewar wadannan abubuwa. Saboda haka duk wasan da bai buga ba za mu yi kewarsa."
A wata sanarwa da ta fitar, Tottenham ta ce: "Muna tabbatar da cewa Harry Kane ya ji rauni a gwiwarsa ta hagu yayin wasanmu da Southampton a ranar sabuwar shekara.
"Tawagar likitocinmu za ta ci gaba da duba matsalar yayin da yake karbar kulawa."
Kane ya ci kwallo 27 a wasa 31 da ya buga a kakar bana - a Tottenham da kuma Ingila.










