Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Southgate, Pogba, Sterling, Simeone da Sancho
Manchester United za ta koma wa kocin Ingila Gareth Southgate idan ta har ta yanke shawarar korar Ole Gunnar Solskjaer a karshen kaka. (Sun)
Mataimakon manajan United Mike Phelan ya ce kulub din na bukatar manyan 'yan wasa. (Evening Standard)
Chelsea a shirye ta ke ta ware makudan kudi domin karbo matashin dan wasan Ingila daga Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 19. (Goal)
A ranar Alhamis Chelsea za ta san ko wa'adin haramta mata sayen 'yan wasa da zai kawo karshe a Fabrairu zai ba ta dama ta yi cefane a Janairu. (Daily Telegraph)
Manajan Real Madrid Zinedine Zidane har yanzu yana sha'awar karbo dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba, mai shekara 26, zuwa Bernabeu. (Marca)
Manchester City tana da tabbacin kan Raheem Sterling, mai shekara 24, zai sabunta kwangilar shi wanda zai kasance dan wasan da ya fi albashi mai tsoka. . (Metro)
Liverpool da Arsenal sun shiga hamayya da Barcelona kan dan wasan Jamus mai shekara 17 dan asalin Najeriya Karim Adeyemi wanda kungiyar Liefering ta Austria ta karba aro daga RB Salzburg. (Sport via Mirror)
Atletico Madrid ta amince ta biya fam miliyan £25.4 kan matashin dan wasan tsakiya Bruno Guimaraes da ke taka leda a kulub din Brazil Athletico Paranaense. (UOL, in Portuguese)
Tottenham za ta iya karbo aron Giovani Lo Celso daga Real Betis - za ta kuma iya sayen dan wasan a Janairu kan fam miliyan £27.3. (ABC de Sevilla via Football London)
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone, wanda a baya ake tunanin zai koma Everton, yana dab da barin Madrid. (Marca via Sport Witness)