Premier League: Watford ta kori kocinta Sanchez Flores

An wallafa

Kungiyar Watford ta kori mai horarwarta Quique Sanchez Flores biyo bayan kashin da ta sha 1-2 a hannun Southampton jiya Asabar a wasan Premier mako na 14.

Watford ta kara da cewa za a nada sabon koci nan take. Sai dai Chris Hughton ne ake sa ran zai gaje shi.

An sake bai wa Sanchez Flores aikin horar da Watford ne ranar 7 ga watan Satumba, inda ya maye gurbin Javi Gracia, bayan ya jagoranci kungiyar a kakar 2015-2016.

Sai dai wasa daya kacal ya ci a cikin 10 da ya buga na Premier, yayin kulob din yake karshen teburi yanzu haka.

"Quique mutumin kirki ne kuma a bayyana take irin kokarin da ya yi na ciyar da kungiyar gaba, amma sakamakon da muke samu su ne suka saka mu daukar matakin," shugaban kungiyar Scott Duxbury ya bayyana.

"Nan gaba kadan za mu nada sabon koci kuma ganin cewa kusan kashi biyu cikin uku na kakar bana ne kawai ya rage, za mu yi bakin kokarinmu domin samun nasara a watanni masu zuwa," in ji shi.

Watford tana da maki takwas a wasa 14 da ta buga kuma maki shida ne kacal tsakaninta da barin gasar Premier - wannan ce kakar Premier mafi muni da ta taba fuskanta.