Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Unai Emery: Dalilai 5 da suka sa Arsenal ta kori Emery
Arsenal ta tsinci kanta a halin kakanikayi tun bayan zuwan mai horaswa Unai Emery, kuma tuni ta bayar da sanarwar korar kocin nata tare da maye gurbinsa da tsohon dan wasanta Freddie Ljungberg.
Duk da cewa kungiyar ta jima tana hakuri da halin da take ciki musamman a lokacin Arsene Wenger, sha'anin ya kazanta a lokacin Emery.
Imam Saleh ya bayyana dalilai biyar da suka sa Emery ya rasa aikinsa:
1. Babu wata kungiya da magoya bayanta da za su lamunci rashin nasara a wasanni bakwai a jere musamman a wannan kaka da kungiyoyi ke rigegeniyar dawo da martabarsu.
Misali shi ne, kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya jagoranci kungiyar a kakar bara har zuwa gasar Champions League, sannan kungiyar ta shafe tsawon shekaru ba tare da ta tsallake mataki na hudu a tebur ba, amma saboda rashin tabuka wani abin kirki a bana ya sa kungiyar ta sallame shi.
2. A tarihin kwaca-kwacan da Arsenal ta yi, Emery ne kadai ya taba samun damar sayan dan kwallo mafi tsada, Niclolas Pepe, kan kudi sama da yuro miliyan 70.
Sai da masu kungiyar suka takarkare duk da mammakonsu sannan suka ba shi damar sayan dan wasan. Sai dai kash, sai ya rika ajiye shi a benci. - ina amfanin sayen dan wasa mai daraja irin wannan alhalin ka san ba za ka rika ba shi dama ba!
3. Ana ganin cewa rashin jituwar da ke tsakanin Emery da kwararren dan wasan tsakiya Mesut Ozil ta shafi aikinsa a matsayinsa na koci.
Duniyar kwallon kafa ta yi amannar cewa Mesut Ozil na sahun gaba a jerin 'yan wasa da ke da kwarewar kara wa kowacce tawaga kuzari a duniya ba ma Arsenal kawai ba, amma sai ya rika ajiye shi a benci.
Da yawan magoya bayan Arsenal sun fara jin haushin Emery ne saboda wannan, sun kuma mara wa Ozil baya saboda suna ganin cewa Emery yana kokarin sallamar Ozil ne daga kungiyar.
4. Kazalika kan 'yan wassan Arsenal bai hadu ba wurin nada wanda zai rika jagorancin Arsenal a cikin fili wato kyaftin.
Abin da mutane ba su sani ba shi ne wasu daga cikinsu suna goyon bayan Mesut Ozil ne kafin Emery ya yanke shawarar bai wa Granit Xhaka, wanda shi kuma ya bata wa magoya baya rai bayan an yi canjinsa kuma hakan ya sa aka karbe daga hannunsa.
A lokaci guda kuma aka nada Pierre-Emerick Aubameyang a matsayin kyaftin din na Arsenal.
5. Zuwansa ke da wuya ya sauya tsarin bayar da horo a sansanin atasayen 'yan wasa, abin da ya kara wa 'yan wasa nauyi kan wanda suka saba dauka a baya.
Ya bijiro da sababbin tsare-tsare na gudu da zagaye fili masu tsanani sabanin yadda tsarin yake a baya, hakan ya shafi wasanninsu na karshen mako da suke a gasar Premier.
A 'yan kwanakin nan kuma, kamar yadda jaridar Evening Standard ta ruwaito, 'yan wasan Arsenal sun rika tsokana tare da yi wa kocin nasu ba'a a fili.
Jaridar ta ce yayin da suke kan hanyar koma wa Ingila daga canjaras din da kungiyar ta yi da Vitoria Guimareas 1-1 a gasar Europa a farkon watan Nuwamba, Emery shiu kadai ya zauna a cikin jirgi yana ta tunane-tunane.
Kuma an jiyo 'yan wasan suna tambaya "wai kyatin nawa gare mu ne" - suna magana kan nada Aubameyang a matsayin kyaftin cikin 'yan kwanaki bayan tube Xhaka.