Champions League: Kungiyoyi takwas ne suka tsallaka zagaye na 16

Asalin hoton, Darren Walsh
A makon nan an samu karin kungiyoyin da suka samu wuri a sauran gurabe 13.
Rukuni na daya da na biyu tuni kungiyoyinsu biyu suka fito.
PSG da Real Madrid sune suka fito a rukunin farko, sai Bayern Munich da Tottenham da suka samu damar tsallakawa zagayen na 16 daga rukuni na biyu.
Manchester City, Juventus, Barcelona da RB Leipzig kowannensu ya samu nasarar fitowa daga rukuni.
Hakan ya nuna cewa kungiyoyi takwas ne suke da gurbi a zagayen na 16 a gasar.
Idan har Chelsea ta samu nasara a wasanta da zata yi da Lille zata samun gurbi a zagaye na gaban. Kungiyoyin Ingila hudu ne kenn suka tsallaka zagaye na gaban.
Chelsea dai tayi canjaras a wasanta da tayi da Valencia da ci 2-2 inda take a mataki na uku a saman teburi yanzu haka.
Itama dai Liverpool abinda take nema yanzu shine samun galaba a kan Salzburg ko kuma canjaras a wasan da za suyi nan gaba, duk da cewa tana saman teburi da maki 10.
Napoli ta gaza samun nasara a wasanni bakwai a jere karon farko tun bayan watan Fabrairu zuwa Maris din shekarar 2013.










