Thierry Henry ya zama sabon kocin Montreal

An wallafa

Thierry Henry, mai shekara 42, wanda ya kwashe shekara hudu da rabi tare da kungiyar Red Bulls da ke New York kafin ya kare aikinsa a 2014, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu tare da zabin karin watanni 12.

Bayan amincewa da komawarsa, Henry ya ce: "Abin alfahari ne ya horar da Montreal Impact."

"Domin kasancewa a Quebec, wato a Montreal, wanda ke dauke da dimbin al'adun, abin mamaki ne. Na dade ina sanya ido akan kulob din, kuma yanzu gashi na samu damar da nake so".

Shugaban Montreal Kevin Gilmore ya ce: "Muna matukar farin cikin sanar da nadin jigon wanda ya iya bayar da gudunmawa a harkar kwallon kafa.

"Henry zai kawo ci gaba sosai a kulob dinmu. Yana da hangen nesa sosai kuma ina ganin zai ba da gudunmawa don ganin wannan kulob din ya cimma burin da muke fata.

"Jagora ne wanda ya tabbatar da kansa a cikin ayyukansa. Kuma muna fata zai nuna mana kwarewar aikinsa a Montreal."

Bayan ya yi ritaya, Henry ya dauki lokaci yana koyarwa a kwalejin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma ya kasance mataimaki ga Roberto Martinez.

Ya fara aiki da kulob din Monaco a kakar bara, amma wasanni hudu ya samu nasara a kai a cikin 20 da kungiyar ta fafata, sai dai kungiyar ta kore shi bayan wata uku da fara yin aiki da ita.

Tsohon dan wasan da ya ciyowa Arsenal da kuma Faransa kwallaye za a gabatar da shi a ranar Litinin mai zuwa.

Zai fara aikinsa ne a hukumance a watan Janairu kafin fara gasar MLS ta shekarar 2020.