Spain ta samu gurbin shiga gasar Euro 2020

An wallafa

Tawagar kwallon kafar Spaniya ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020, bayan da ta tashi 1-1 da Sweden ranar Talata.

Spaniya wadda ke rike da kofin nahiyar Turai uku na neman maki daya tal ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai tun kan karawa da Sweden.

A kuma karawar Sweden ce ta fara cin kwallo ta hannun Marcus Berg, daga baya Spaniya ta farke daf da za a tashi daga fafatawar ta hannun Rodrigo.

Golan Spaniya David de Gea ya hana wani kwallon da Robin Quaison ya sawa kai, kan ya yi rauni a canja shi.

Ita ma Spaniya ta samy damarmakin zura kwallaye a raga, inda mai tsaron ragar Sweden, Robin Olsen ya tare kwallon Rodri da Ruiz da kuma ta Gerard Moreno.

Tawagar kwallon kafar Spaniya ta zama ta shida da ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020, bayan Belgium da Italia da Rasha da Poland da kuma Ukraine.