Kila a buga El Clasico a Real, maimakon Camp Nou

Asalin hoton, Getty Images
Mahukuntan gasar La Liga sun bukaci da a dauke wasan hamayyar da Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid zuwa Santiago Bernabeu maimakon Camp Nou.
A ranar 26 ga watan Oktoba aka tsara cewar Real Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na tara a gasar cin kofin La liga a karawar hamayya da ake kira El Clasico.
Sai dai kuma ana ta yin zanga-zanga a Barcelona, bayan da aka daure shugabannin Catalonia tara ranar Litinin.
Ana kuma sa ran ci gaba da karin zanga-zanga a filayen wasannin tamaula.
Mahukuntan La Liga sun bukaci hukumar kwallon kafar Spaniya da ta janye wasan daga Barcelona zuwa Real Madrid, inda ta ce tana tsoron tashin rikicin da zai iya fin karfinta.
BBC ta nemi ji daga kungiyoyin biyu don karin bayani sai dai ta fahimci cewar ba a tuntube su ba kan batun.
Ana sa ran za a tuntubi kungiyoyin biyu nan gaba don ji shawara daga wajen su kafin hukumar kwallon kafar Spaniya ta yanke hukunci a mako mai zuwa.
Hukumar kwallon kafar Catalonia ta dakatar da dukkan wasu wasannin kwallon kafa a yankin a ranar Litinin, amma hakan bai shafi karawar La Liga ba.











