Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za su fafata da Juventus kan Dambele, Lazio 'na nuna wariyar launin fata'
Tsohon dan wasan Ingila Steven Caulker, wanda ya buga tamaula a Dundee na dan wani lokaci bara, ya ce zai yi mubaya'a ga Scotland kuma har ya kira wo mataimakin kocin kungiyar kwallon kafar kasar Steven Reid don bayyana masa matsayinsa. Kakar dan wasan mai shekara 27, wanda a yanzu yake buga wa Turkiyya kwallo, 'yan kasar Scotland ce kuma sau daya ya buga wa Ingila tamaula a wasan sada zumunta. (Herald)
Celtic sun yi wa magoya bayansu alkawarin cewa za su zage dantse wajen ganin an ba su damar buga wasa a kan lokaci bayan da suka amince cewa basu ji dadi kan yadda aka sanya wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin Betfredda suka fafata da Hibernian F.C. a watan Nuwamba, da ma wasan lig da suka kai ziyara Ross County a watan Disamba. (Daily Record)
Tsohon mai tsaron ragar Rangers Andy Goram ya yi amannar cewa akwai bukatar kulob din ya mayar da hankali wurin sabunta kwantaragin Allan McGregor, mai shekara 37. (Daily Record)
A shirye Arsenal suke su fafata da Juventus da kuma Paris St-Germain wajen zawarcin dan wasan Celtic mai shekara 16 Karamoko Dembele. (Sun)
Uefa ta tuhumi Lazio a kan zargin nuna wariyar launin fata abin da zai iya kai wa ga rufe wani bangare na filin wasansu kuma hakan wani koma-baya ne ga kulob din wanda ke shirin karbar tikiti 9000 wajen karbar bakuncin gasar Europa ranar bakwai ga watan Nuwamba. (Daily Record)
Dan wasan tsakiya naScotlandKenny McLean ya kwatanta bajintar da Lawrence Shankland ya yi tun da ya komo murza leda da irin wacce takwaransa a Norwich Teemu Pukki ya yi. (Daily Record)
An gayyaci shugaban Russia Vladimir Putin domin yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa shekara 67 a filin wasan Luzhniki ranar Alhamis lokacin da Scotland za su je domin fafatawa a neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai ta 2020. (Sun)
Aberdeen ba za su daukaka kara kan jan katin da aka bai wa Curtis Main da Lewis Ferguson ranar Asabar ba a wasan da suka tashi da ci 1-1 da Hibernian F.C. (Daily Record)