Babu Bale da James a tawagar Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid tana shirin karawa da Club Brugge a wasan rukuni na gasar Zakarun Turai ta Champions League da karfe 5:55 na yammacin yau Talata.
Real tana kokarin kauce wa rashin nasara uku a jere a gasar a tarihin kungiyar bayan Ajax ta doke ta a watan Maris da kuma lallasawar da PSG ta yi mata mako uku da suka gabata.
Babu Gareth Bale da James Rodriguez a cikin tawagar da za ta yi fafatawar amma Isco da Marcello sun dawo fili kuma Zidane ya saka su a cikin tawagar.
Kazalika, su ma 'yan wasa Rodrygo Goes da Alvaro Odriozola da Brahim Diaz da kuma Mariano ba a saka su cikin tawagar ba.
Zidane ya ajiye Bale ne domin ba shi hutu saboda tsoron rauni bayan ya sha fafatawa a manyan wasanni tsakanin Sevilla da kuma Atletico Madrid.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Sauran wasan da za a yi a rukunin A shi ne tsakanin PSG ta kasar Faransa da Galatasaray ta kasar Turkiyya.
PSG ce a saman teburin da makinta uku sai kuma Real Madrid wadda ke kasan teburin wacce ba ta da maki.
"Har yanzu ban zama Galactico ba"

Asalin hoton, Getty Images
Eden Hazard, wanda yake cikin tawagar da za ta fafata a yau, ya ce ba ya cikin tawagar taurarin 'yan wasan Madrid da ake kira Galactico.
Galacticos kalma ce ta Sifaniyanci da ke nufin fitattu. Zarata cikin fitattun 'yan wasa a duniyar kwallon kafa su ake kira Galacticos.
Galacticos a Real Madrid su ne 'yan wasan kwallon kafa mafiya tsada a duniya.
Hazard ya koma Madrid kan kudi fan miliyan £89, sannan ya gaji jesi mai lamba 7, abin da ke nuni da cewa shi ne magajin Cristiano Ronaldo.
"Ni ba Galactico ba ne ba tukunna. Amma lalllai zan nuna cewa zan iya shiga cikinsu," in ji Hazard.
"Muna sane da tarihin lamba 7 a kungiyar nan kuma ina so na zama mafi kwarewa a duniya. Zan so in bai wa kulob din komai da komai, ba a cikin wasanni ba kawai har da atasaye."
Dan wasan mai shekara 28 ya buga wasa ukun na La Liga na farko amma har yanzu bai ci kwallo ko daya ba kuma bai taimaka an ci ko daya ba.
Wasan farko da ya buga wa Madrid a Champions League da rashin nasara ya kare a hannun PSG da ci 0-3, inda ya buga shot daya kacal.











